Tinubu na Shirin Garambawul, Wani Jigo Ya Yi Magana kan Ministocin da Za a Kora
- Daniel Bwala ya bayyana cewa babu wanda ya san ministocin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai kora a garambawul da yake shirin yi
- Tsohon kakakin kwamitin kamfen PDP ya ce duk wanda ya yi iƙirarin ya sani zato kawai yake yi ko kuma bai san abin da yake yi ba
- Bwala ya kuma yi tsokaci kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa da yiwuwar shi zai maye gurbin kakakin shugaban ƙasa da ya yi murabus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon kakakin kwamitin kamfen Atiku Abubakar a zaɓen 2023, Daniel Bwala ya yi tsokaci kan garambawul da shugaban kasa Bola Tinubu ke shirin yi.
Bwala ya bayyana cewa shugaban kasa ne kaɗai ke da ikon yanke ministocin da zai sallama daga aiki da waɗanda zai ci gaba da tafiya da su a gwamnatinsa.
Daniel Bwala ya faɗi haka ne a cikin shirin safe na gidan talabijin na Channels tv yau Alhamis, 26 ga watan Satumba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane ministoci Tinubu zai kora?
Tsohon jigon PDP ya ce duk wanda ke ikirarin ya san ministocin da za a kora ko waɗanda za su zauna zato kawai yake amma bai san komai ba.
A rahoton Vanguard, Bwala ya ce:
"Shugaban ƙasa yana tantance waɗanda suka yi imani da gwamnatinsa saboda duk wanda ya aminta da ita zai zama kamar ɗan aikenta ne.
"Dangane da waɗanda za a kora da waɗanda za su zauna wannan haƙkin shugaban ƙasa ne, shi kaɗai ya san su wa zai kora da waɗanda zai ci gaba da aiki da su.
"Duk wanda ya ce ya san (ministocin da za a kora) to ko dai yana zato ne ko kuma mutumin ko waye shi bai yi wa kansa adalci ba."
Tinubu na shirin naɗa Bwala a muƙami?
Bayan murabus din Ajuri Ngelale daga mukamin mai magana da yawun shugaban ƙasa, an fara raɗe-raɗin watakila Tinubu ya maye gurbina da Bwala.
Da yake mayar da martani game da jita-jitar da ake yadawa cewa zai maye gurbin Ngelale, Bwala ya ce:
“Ban san meyasa mutane suke jingina ni da aikin ba. Abin da na sani duk wanda ya amince da gwamnati zai ba da gudummuwa da goyon baya a ko ina yake, abin da nake yi kenan, ba dole sai ina da muƙami ba."
An taso Tinubu kan shirin korar ministoci
A wani rahoton kuma ƴan siyasa da dama sun fara kama kafa tun bayan fitar da rahoto cewa Bola Tinubu ya shirya sallamar wasu ministocinsa.
Wasu daga cikinsu sun fara neman yadda za a yi yaransu su tsallake wannan sauye-sauye da za a yi a gwamnatin Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng