Gwamnatin Tinubu Ta Taso Tsohon Gwamna a Arewa, Ana Zargin Ya 'Sace' N110bn

Gwamnatin Tinubu Ta Taso Tsohon Gwamna a Arewa, Ana Zargin Ya 'Sace' N110bn

  • Gwamnatin Tarayya ta hannun EFCC ta sake bankaɗo wata almundahana ta N110bn da take zargin da hannun Yahaya Bello
  • Lauyoyin EFCC sun shigar da sababbin tuhume-tuhume 16 kan tsohon gwamnan na Kogi a gaban babbar kotun Abuja
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ya ke ci gaba da gujewa EFCC tare da ƙin halartar zaman kotu kan tuhumar wawure N80.2bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalain arzkin ƙasa zagon ƙasa watau EFCC ta sake taso tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da sababbin tuhume-tuhume.

Duk da ba a gama da shari'ar da ake tuhumarsa da wawaure N80.2bn ba, EFCC ta sake shigar da ƙarar tsohon gwamnan tana zarginsa da yin sama da faɗi da wasu N110bn.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya gaji da matsin lambar EFCC, ya roƙi Tinubu Alfarma

Yahaya Bello.
Gwamnatin tarayya ta shigar da sababbin tuhume-tuhume 16 kan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

EFCC ta sake taso Yahaya Bello

Daily Trust ta tattaro cewa EFCC ta ƙara zargin Yahaya Bello da aikata laifuffuka 16 da suka shafi cin amana da safarar kudi a gaban babbar kotun Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya ce ta shigar da wannan sabuwar ƙara kan Yahaya Bello ta hannun lauyoyin EFCC, Kemi Pinheiro SAN, Rotimi Oyedepo SAN da wasu lauyoyi shida.

Sababbin tuhume-tuhumen na zuwa ne a lokacin da tsohon gwamnan ke ci gaba da wasan ɓuya da ƙin halartar zaman babbar kotun tarayya, inda ake tuhumarsa da satar N80.2bn.

EFCC: Laifukan da ake zargin Yahaya Bello

A takardar sabuwar ƙarar da The Cable ta ci karo da ita, EFCC ta ce ta gano wani sabon rashin gaskiyar da Yahaya Bello ya tafka lokacin yana mulkin Kogi.

A cewar hukumar EFCC, ta bankaɗo wata badaƙala da take zargin da hannun Yahaya Bello a zambar makudan kuɗi da suka kai N110,446,470,089.00.

Kara karanta wannan

Ana batun zaben Edo, an fara shirin dakatar da gwamna daga jam'iyya

Wani sashen takardar ƙarar ya ce:

"A wani lokaci a 2016, kai Yahaya Adoza Bello, Umar Shu'aibu Oricha da Abdulsalami Hudu kun haɗa baki wajen aikata haramtaccen aiki da ya saɓa doka, ku ka wawure N110,446,470,089.00 da aka baku amana."

EFCC ta yi yunkurin cafke Yahaya Bello

A wani rahoton kuma, hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta yi karin haske kan yunkurin kama Yahaya Bello da aka yi.

EFCC ta zargi gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo da boye Yahaya Bello yayin da jami'anta suka yi yunkurin cafke shi a kwanakim baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262