"Mun Gano Shirinsa," EFCC Ta Faɗi Dalilin Ƙin Sauraron Yahaya Bello da Ya Miƙa Wuya
- Hukumar EFCC ta bayyana dalilan da ya sa ta ki sauraron tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello lokacin da ya miƙa kansa a makon jiya
- A wata sanarwa da ta fitar, EFCC ta ce ta gano cewa Bello ya yi wani shiri kuma ya zo tare da gwamna mai mai rigar kariya da muƙarrabansa
- Sai dai duk da haka hukumar mai yaki da cin hanci da rashawa ta ce ba za ta haƙura ba har sai ta gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta yi ƙarin haske kan zuwan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ofishinta a makon jiya.
EFCC ta ce ta ƙi sauraron Bello a lokacin da ya miƙa kansa saboda yadda ya riƙa take doka tare da yin abubuwan da za su jawo masa tausayawar ƴan Najeriya.
Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X da yammacin yau Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa EFCC ba ta titsiye Bello ba?
Haka nan kuma EFCC ta ce zuwan Yahaya Bello hedkwatarta tare da wasu mukarrabansa da wani gwamna mai ci na cikin dalilansa na ƙin sauraron shi.
"Har yanzun Yahaya Bello ya gaza zuwa ya kare kansa kan tuhumar da ake yi masa na karkatar da N80.2bn a gaban mai shari'a Nwite.
"Zuwansa hedkwata tare da muƙarrabansa, gwamna mai ci wanda ke da rigar kariya, ƴan midiya da wasu bayanai da EFCC ta tattara a sirrance ya sa aka ki karɓar tayinsa na miƙa wuya
- Hukumar EFCC
"Mun gano shirinsa" - EFCC
EFCC ta ce ta gano tsohon gwamnan ya yi wani shiri a lokacin da ya kawo kansa hedkwatar ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, 2024.
Hukumar ta ci gaba da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa har sai ta tabbatar da tsohon gwamnan ya gurfana a gaban kotu domin fuskantar tuhumar da ake masa.
"Kamata ya yi Yahaya Bello ya maida hankali wajen wanke kansa maimakon wasan ɓuya da ɓaɓatun ana zaluntarsa wanda ba haka ba ne," in jin sanarwar.
Majalisar Kogi ta nemi a sauke shugaban EFCC
A wani rahoton kuma ƴan majalisar jihar Kogi sun bukaci a gaggauta tsige shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede kan rikicin hukumar da Yahaya Bello.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar EFCC ta yi yunkurin kama tsohon gwamna Yahaya Bello a gidan gwamnatin jihar Kogi da ke Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng