Murna Za Ta Koma Ciki: Kungiyar APC na Shirin Daukaka Kara kan Nasarar Ganduje

Murna Za Ta Koma Ciki: Kungiyar APC na Shirin Daukaka Kara kan Nasarar Ganduje

  • Za a sake sabon lale yayin da kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ke shirin komawa kotu kan tsige Abdullahi Ganduje
  • Wannan ya biyo bayan watsi da karar da kungiyar ta shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi bisa wasu dalilai
  • Kotun ta ce kamata ya yi kungiyar da ta bi dukkanin hanyoyin sulhu na jam'iyyarta, kafin garzayowa neman hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Da alama tsuguno ba ta kare ba bayan kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ta ki amincewa da hukuncin babbar kotun tarayya kan nasarar Abdullahi Umar Ganduje a kotu.

Kara karanta wannan

Unga79: Shugaba Tinubu ya koda Najeriya, ya ce Afrika ba ta bukatar tallafi daga kasashe

Kotun ta yi watsi da bukatar kungiyar APC na korar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar bisa dalilin nadi ba bisa ka'ida.

Ganduje
Kungiyar APC za ta koma kotu kan tsige Ganduje daga shugaban jam'iyya Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa an nada Abdullahi Ganduje a mukamin shugaban jam'iyya bayan Abdullahi Adamu ya yi murabus a watan Yuli, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje: Dalilin rikicin cikin gidan APC

Tsohon shugaban APC na kasa kafin Abdullahi Umar Ganduje, Abdullahi Adamu ya fito daga jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya.

Wasu daga cikin yan jam'iyyar na adawa da maye gurbinsa da Ganduje, wanda ya fito daga Arewa ta Yamma, a maimakon a nemo wani daga shiyyar da tsohon shugaban ya fito.

Me yasa kotu ta ba Ganduje nasara?

Mai Shari'a Inyang Ekwo ya kori karar da aka shigar gabansa bisa zargin cewa kungiyar APC da ta shigar da karar ba ta da rajista da hukumomin da su ka dace.

Kara karanta wannan

Zargin almundahana: Kotu ta dage shari'ar Yahaya Bello zuwa 30 oktoba

Sannan, alkalin ya ce akwai matakan mika koke da sulhu na cikin kowace jam'iyya, wanda ya kamata masu shigar da karar su bi kafin zuwa kotu.

Ganduje na samun nasara a jam'iyyar APC

A wani labarin kun ji yadda shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke samun nasarori a matsayinsa da shugaban da wasu a cikin jam'iyyar ke adawa da jagorancinsa.

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kori karar da aka shigar ana neman tsige Ganduje daga kujerarsa, sannan ya yi nasarar kawo kujerar gwamnan jihar Edo a makon da ya wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.