Rikicin NNPP: Ƴan Majalisa 2 Sun Fice daga Jam'iyyarsu Kwankwaso, Sun Koma APC

Rikicin NNPP: Ƴan Majalisa 2 Sun Fice daga Jam'iyyarsu Kwankwaso, Sun Koma APC

  • Rigingimun cikin gida a NNPP ne ya jawo ƴan majalisa biyu suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Nasarawa
  • Ƴan majalisar dai sun ce ba za su iya ci gaba da zama a NNPP ba saboda yadda ta dare gida biyu kuma kowane ɓangare na da tambari
  • NNPP ta reshen Nasarawa ta kafa kwamiti domin ya gudanar da bincine kan sauya shekar ƴan majalisa kuma ya miƙa rahoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Jam'iyyar NNPP ta rasa ƴan majalisa biyu da take da su a zauren majalisar dokokin jihar Nasarawa saboda rikicin cikin gida a matakin ƙasa.

Ƴan majaisar dai sun ce sun sauya sheƙa ne saboda rigingimun cikin gida wanda ya raba NNPP gida biyu, daga ciki sun ambaci cewa tana da tambari biyu.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta fara tantance sabuwar shugabar alƙalan Najeriya, an samu bayanai

Kwankwaso da tambarin NNPP.
NNPP ta rasa ƴan majalisa 2 da take da su a Nasarawa saboda rikicin cikin gida Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa ƴan majalisar sune Mohammed Garba Isimbabi mai wakiltar Toto/Gadabuke da Musa Abubakar Ibrahim mai wakiltar Doma ta Kudu duk a Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƴan majalisar suka bar NNPP?

A cewarsu rikicin cikin gidan ya kai ga raba NNPP gida biyu kuma kowane ɓangare na da tambarinsa, ga kuma yawan kararraki a gaban kotu.

Yayin da Garba Isimbabi ya sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa APC a ranar 21 ga watan Agusta, Musa Abubakar ya bi sahunsa a makon jiya inji rahoton Pulse.

Bayan wannan sauya sheƙa, ƴan majalisar APC a majalisar dokokin jihar Nasarawa suka karu daga 10 zuwa 12, PDP na da tara, sai kuma SDP da take da mutum uku.

Kwamitin da NNPP ya kafa ya miƙa rahoto

Wannan ne ya sa jam’iyyar NNPP reshen jihar ta kafa wani kwamiti mai mutane biyar da zai binciki dalilan da suka sa ‘yan majalisar suka sauya sheƙa.

Kara karanta wannan

Kano: NNPP ta samu karuwa, yan jam'iyyun adawa 30 sun rungumi Kwankwasiyya

Rahoton kwamitin, wanda aka gabatar a ranar 21 ga Satumba, ya bayyana cewa ƴan majalisar sun ɗauki matakin komawa APC ne saboda rikicin NNPP a matakin ƙasa.

"Mun gano cewa akwai rabuwar kan da suka kafa hujja da shi a NNPP ta ƙasa, dan haka ba su yi kuskure ba," in ji rahoton.

Jaruman Kannywood sun koma APC

A wani labarin, siyasar Kano na cigaba da daukan hankulan al'ummar Arewacin Najeriya yayin da ake cigaba da samun masu sauya sheka a jihar.

A wannan karon, an samu wasu daga cikin jaruman Kannywood da suka ajiye tafiyar Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262