"Ƴan Najeriya Za Su Amfana," Wasu Manyan Sarakuna Sun Goyi Bayan Tsare Tsaren Tinubu

"Ƴan Najeriya Za Su Amfana," Wasu Manyan Sarakuna Sun Goyi Bayan Tsare Tsaren Tinubu

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara samun karɓuwa a wurin sarakunan gargajiya na yankin Neja Delta a Najeriya
  • A wurin taron masu ruwa da tsaki, sarakunan sun bayyana cikakken goyon bayansu ga tsare-tsaren da ya ɓullo da su
  • Manyan kasar sun kuma yabawa shugaba Tinubu bisa naɗa ɗansu a matsayin wanda zai jagorancin shirin afuwa PAP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Sarakunan gargajiya daga yankin Neja Delta sun bayyana cikakken goyon bayansu ga manufofin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sarakunan sun ce suna goyon bayan tsare-tsaren da shugaban ƙasa ya ɓullo da su da nufin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Sarakunan yankin Neja Delta sun jaddada goyon bayansu ga Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Getty Images

Sun sanar da matsayarsu ne a wurin taron masu ruwa da tsaki wanda shirin afuwa na ofishin shugaban ƙasa (PAP) ya shirya a Warri, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kara samun nasara, sun hallaka gawurtaccen ɗan bindiga a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufofin Tinubu za su amfani al'umma

Sarkin Tuomo, Mai martaba F. F. Tabai tare da wasu sarakuna sun bayyana kwarin gwiwarsu dangane da matakan da shugaban ya dauka a kan yankin Neja Delta.

A cewar sarakunan, shirye-shiryen da Shugaba Tinubu ya ɓulllo da su a yankin zai amfanar da al'ummarsu ta ɓangarori daban-daban.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun PAP, Mr. Igoniko Oduma ya fitar bayan kammala taron ranar Talata.

Bugu da ƙari, sarakunan sun ƙara jaddada gudummuwar da suke bayar wa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Neja Delta, rahoton The Nation.

Sarakunan sun yabawa Bola Tinubu

Da yake jawabi a madadin sarakunan, Sarki Tabai ya ce:

"Muna godiya ga mai girma shugaban ƙasa bisa naɗa ɗanmu a matsayin wanda zai jagoranci shirin PAP, muna tabbatar masa da za mu mara masa baya.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin gwamna na shirin sauya sheƙa, ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP

"Za mu yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa shugaban kasa ya yi nasara, mutanen mu su ne za su sha romon tsare-tsaren da ya zo da su."

Tinubu ya buƙaci majalisa ta amince da naɗin CJN

A wani labarin, Bola Ahmed Tinubu ya aika saƙo ga majalisar dattawa yana neman ta amince da naɗin Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alkalai (CJN).

A watan jiya ne shugaban ƙasar ya naɗa ta a matsayin CJN ta riko bayan bayan Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262