Damagum: Jerin Gwamnoni 6 da Ke Goyon bayan a Tsige Shugaban PDP na Kasa
- Gwamnonin da aka zaba a karkashin PDP sun raba gari kan bukatar Umar Damagum ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar na kasa
- Damagum ya maye gurbin Iyorchia Ayu a cikin Maris 2023, sai dai a yanzu yana fuskantar barazanar sauke shi daga wannan mukami
- A halin yanzu, Damagum na fuskantar matsin lamba daga wasu gwamnoni shida, wadanda ke ganin lokaci ya yi ya sauka daga shugaban PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Rahotanni sun ce akalla gwamnonin PDP shida ne ke adawa da Umar Damagum kan ya ci gaba da zamansa shugaban jam’iyyar na kasa.
A kwanakin baya ne dai aka bayyana cewa 'yan kwamitin ayyukan PDP na kasa (NWC) da mataimakansu sun yi yunkurin tsige Damagum.
Rikicin shugabancin jam'iyyar PDP
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito a baya-bayan nan, a cikin gwamnonin da ke adawa da Damagum akwai Sanata Bala Mohammed, shugaban kungiyar PDP na kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan dai za a iya tunawa a watan Agusta ne Damagum ya ce fafutukar da ya ke yi na ci gaba da zama a ofis ba 'a mutu ko a yi rai' ba ne a wajen shi.
Wannan ya biyo bayan yadda wasu jiga-jigan jam’iyyar suka nuna cewa Damagum, haifaffen jihar Yobe ya riga ya wuce gona da iri a shugabancin rikon kwarya da aka ba shi.
Sai dai shugaban PDP na kasar da ke cikin takun-saka da manyan gwamnoninsa ya ce sauya shugabanni ko akasin hakan ba zai kwace matsayinsa a jam'iyyar ba.
Gwamnonin PDP 6 masu adawa da Damagum
Ga jerin gwamnoni 6 da suka amince a tsige Umar Damagum daga matsayin shugaban PDP na kasa:
- Bala Mohammed (Bauchi)
- Godwin Obaseki (Edo)
- Douye Diri (Bayelsa)
- Siminalayi Fubara (Rivers)
- Umo Eno (Akwa Ibom)
- Sheriff Oborevwori (Delta)
Matsayar Atiku kan shugaban jam'iyyar PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya tsoma baki a rikicin jam'iyyar musamman kan shirin tsige Umar Damagum.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fara tuntubar wasu 'yan kwamitin NWC da ke son Damagum ya bar shugabancin PDP tare da nuna goyon bayansa kan wannan shiri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng