Ana Raɗe Raɗin Gwamna na Shirin Sauya Sheƙa, Ciyamomi Sun Fice daga Jam'iyyar PDP
- Rahotanni sun nuna kantomomin da Gwamna Siminalayi Fubara ya nada sun fara barin jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Ribas
- Hakan na zuwa ne bayan jita-jita ta fara yawo cewa shi kansa gwamna yana shirye-shiryen sauya sheƙa saboda rikicinsa da Nyesom Wike
- Sai dai a lokacin da ya karɓi baƙuncin ƴan majalisar amintattun PDP kwanakin baya a Fatakwal, Fubara ya ce yana nan daram a jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi na riƙon ƙwarya waɗanda Gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa a jihar Ribas sun fice daga PDP.
Rahotanni sun nuna kantomomin sun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APP a lokacin da ake shirye-shiryen zaben kananan hukumomi ranar 5 ga watan Oktoba, 2024.
Punch ta tattaro cewa an fara yaɗa jita-jitar cewa Gwamna Fubara na shirin jefar da PDP, ya koma jam'iyyar APP saboda rikicinsa da ministan Abuja, Nyesom Wike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba alaƙar Fubara da magabacinsa kuma tsohon ubangidansa Wike ta yi tsami wanda ya haifar da rikicin siyasa a jihar Ribas.
Gwamna Fubara ya musanta shirin barin PDP
Duba da yadda alamu suka nuna Wike ya karɓe ragamar PDP reshen jihar Ribas, ana fara raɗe-raɗin Gwamna Fubara na shirin sauya sheka zuwa APP.
Sai dai a lokacin da ya karɓi bakuncin ƴan majalisar amintattun PDP a Fatakwal, Gwamna Fubara ya musanta duk wata jita-jitar sauya sheƙa.
Amma a halin yanzu, wasu kantomimi na tsagin gwamnan tare da magoya bayansu sun fara fita daga PDP suna haɗewa da jam'iyyar APP, rahoton The Cable.
Ƴan tsagin Fubara sun tsaya takara a APP
Kusan dukkan ƴan takarar ciyamomi da kansiloli na tsagin Gwamna Fubara sun fara shirye-shirye ne a ƙarƙashin inuwar APP duk da cewa an fara yaƙin neman zaɓe.
Tuni dai fastocin kantoman ƙaramar hukumar birnin Fatakwal, Ezebunwo Ichemati da tambarin kamfen APP suka fara yawo a kwaryar birnin.
Da yake jawabi kwanan nan, Ichemati ya yi alkawarin samar da sahihin jagoranci ga al'umma idan aka zabe shi a matsayin shugaban ƙaramar hukumar birni.
Ƴan majalisar 27 sun yi nasara a kotu
A wani rahoton kuma kotu ta kori ƙarar da aka nemi maye gurbin ƴan majalisar dokoki 27 da ke goyon bayan Nyesom Wike a rikicin jihar Ribas.
Jam'iyyar APP ta kai ƙarar ƴan majalisar dokokin bisa sauya shekar da suka yi daga PDP zuwa APC, inda ta nemi a maye gurbinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng