Masu Sa Ido Sun yi Watsi da Zaben Edo, Sun Zargi INEC

Masu Sa Ido Sun yi Watsi da Zaben Edo, Sun Zargi INEC

  • Wasu kungiyoyi da suka saka ido a zaben Edo sun fitar da rahoto kan yadda zaben ya gudana da yadda aka tatttara kuri'u
  • Kungiyoyin sun ce zaben bai cika sharudan ingantaccen zabe ba kuma sun zargi hukumar INEC da karya dokokin zaɓe
  • An ce an samu wasu jami'an tsaro sun wuce gona da iri wajen tattara sakamako da aka yi bayan an gama ka da kuri'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Wasu kungiyoyin sa ido sun fitar da rahoton bayan zabe a kan zaben Edo da ya gudana a ranar Asabar da ta wuce.

Kungiyoyin sun ce an samu abubuwan da suka shafi ingancin zaben kuma sun zargi hukumar INEC da karya doka.

Kara karanta wannan

"Ba a yi mana adalci ba:" Jam'iyyar LP ta fadi wanda ya ci zaben Edo

Zaben Edo
Kungiyoyi sun yi watsi da zaben Edo. Hoto: Asue Ighodalo|Monday Okpebholo|Akpata Olumide Anthony
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kungiyoyin sun yi kira na musamman kan matakin da ya kamata hukumomi su dauka a kan zaben Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu sa ido sun yi watsi da zaben Edo

Wasu kungiyoyi da suka sa ido kan yadda zaben Edo ya gudana sun yi watsi da sakamakon da hukumar INEC ta tattara a Edo.

Kungiyoyin sun ce hukumar INEC ta karya dokar zabe ta shekarar 2022 inda suka ce an samu kuri'u mabanbanta a mazabu da wajen tattara kuri'a.

An zargi jami'an tsaro da karya doka

Kungiyoyin sun ce bayan kuskuren da aka samu a bangaren INEC an samu wasu jami'an tsaro da suka wuce gona da iri yayin zaben.

Kungiyoyin sun ce wasu jami'an tsaro sun yi barazana ga jami'an INEC yayin tattara sakamako.

An yi watsi da sakamakon zaben Edo

Kara karanta wannan

Yiaga: Kungiya ta yi fallasa, ta zargi INEC da tafka maguɗi a zaben gwamnan Edo

Kungiyoyin sun ce sun yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ta sanar da ya nuna Monday Okpebholo ne ya yi nasara.

A karkashin haka, kungiyoyin sun bukaci hukumomi su sake bahasi kan zaben domin wanke kansu a idon yan Najeriya.

PDP ta koka kan zaben Edo na 2024

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus ya zargi jami'yyar APC da yaki da demokradiyya a zaben Edo na ranar Asabar.

Secondus ya ce akwai alamun cewa APC na son lalata dimokuraɗiyyar Najeriya wanda ba lallai a samu karfin gwiwar zaben 2027 ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng