'Dan PDP Ya Fashe da Kuka a Bidiyo yayin Hira a Gidan Talabijin kan Zabe
- Bayan sanar da sakamakon zaben jihar Edo, jam'iyyar PDP ta cigaba da kokawa kan yadda aka gudanar da zaben
- Mataimakin daraktan kamfen dan takarar PDP, Asue Ighodalo ya koka kan yadda aka tafka magudi a zaben da aka yi
- Emmanuel Odigie ya fashe da kuka ana tsaka da hira da shi a gidan talabijin inda jagoran shirin ya yi ta rarrashinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Mataimakin daraktan kamfen PDP a jihar Edo, Emmanuel Odigie ya fashe da kuka yayin hira a gidan TV.
Odigie ya nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zaben gwamnan jihar inda Asue Ighodalo ya yi rashin nasara.
Edo: Jigon PDP ya fashe da kuka
Mataimakin daraktan ya fashe da kuka ne yayin hira da Arise TV wanda wakilinsu ya wallafa a shafin X a yau Litinin 23 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Odigie ya gagara rike hawayensa ana tsaka da hirar yayin da ya ke korafi kan rashin nasarar Asue Ighodalo.
Rufai Oseni wanda ke jagorantar shirin ya yi ta kokarin rarrashin dan siyasar amma abin ya ci tura.
"Idan sun yi haka domin kare dan takara mafi kyau da ya ke da kwarewa da tunani da himmatuwa wurin kawo sauyi a jihar Edo, ba zan damu ba ko kadan."
- Emmanuel Odigie
Wanene ya ci zaben gwamnan jihar Edo?
Wannan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta sanar da dan takarar APC a zaben, Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Okpebholo ya samu kuri'u har 291,667 yayin da mai bi masa daga jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 247,244.
Edo: Shaibu ya yi shagube ga Obaseki
Mun ba ku labarin cewa jigon APC kuma mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu ya sake caccakar Gwamna Godwin Obaseki.
Shaibu ya ce ko kadan bai rike Obaseki a zuciyarsa ba duk da abubuwan da suka faru a baya inda ya ba shi shawara.
Ya ce gwamnan bai taba cin zabe ba sai da taimakonsu inda ya ce rasa karamar hukumarsa ya tabbatar da haka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng