Sanatan APC Ya Dura kan Gwamna, Ya Ce Ya Mutu Murus a Siyasar Najeriya

Sanatan APC Ya Dura kan Gwamna, Ya Ce Ya Mutu Murus a Siyasar Najeriya

  • Sanata Adams Oshiomhole ya ce gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya mutu murus a siyasance
  • Oshiomhole, tsohon gwamnan Edo ya ce duk da kalaman Obaseki na a mutu ko a yi rai, al'umma sun fito sun zaɓi Monday Okpebolo na APC
  • Wannan dai na zuwa ne bayan INEC ta bayyana APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan da aka yi ranar Asabar, 21 ga watan Satumba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Tsohon gwamnan Edo kuma tsohon shugaban APC, Sanata Adams Oshiomhole, ya ce Gwamna Godwin Obaseki ya mutu murus a siyasance.

Oshiomhole, Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka kammala.

Kara karanta wannan

'Ba haka ba ne,' Sarkin Benin ya ƙaryata APC kan zargin yaƙar PDP a zaben Edo

Adams Oshiomhole.
Sanata Adams Oshiomhole ya ce sun shafe babin Gwamna Obaseki a siyasance Hoto: Adams Oshiomhole
Asali: Twitter

Da yake hira da Channels tv a shirin siyasa a yau, sanatan ya ce Obaseki ya yi ikirarin wannan zaɓen a mutu ne ko a yi rai, ga shi kuma mutane sun yanke hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba a ranar Lahadin da ta gabata, hukumar zaɓe INEC ta ayyana Monday Okpebolo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

A cewar Adams Oshiomhole, sakamakon zaɓen da INEC ta sanar da ya nuna wanda al'ummar jihar Edo suke buƙatar ya jagorance su.

Sanata Oshiomhole ya yi magana kan zaben Edo

Da aka tambaye shi ko ya damu da kalaman da suka biyo bayan ayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya samu nasara, Oshiomhole ya ce:

"A’a ko kaɗan, mukaddashin shugaban PDP ya yi maganar kare kuri’u da jininsa, saboda mutanen Edo za su sadaukar da jininsu.

Kara karanta wannan

"Za a sharbi romon dimukuradiyya:" Zababben gwamnan Edo ya yi albishir

"Mu muna tare da kalaman tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan wanda ya ce babu zaɓen da ya kai ƙimar jinin ɗan Najeriya guda ɗaya.
"Amma sai ga shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa yana maganar zubda jini saboda zaɓe."

"Mun gama da Gwamna Obaseki a siyasa" - Oshiomhole

Dangane da kalaman Gwamna Obaseki na a mutu ko a yi rai, Adams Oshiomhole ya ce ya kalli hirar za aka yi da gwamnan mai barin gado.

A rahoton Daily Trust, Oshiomhole ya ci gaba da cewa:

"Na saurari hirar da aka yi da shi a Channels yana cewa a mutu ko a yi rai. Lokacin da kuka tambaye shi ya ce idan suka zaɓi wani za su mutu, to yanzu mutanen Edo sun gama aikinsu.
"Ina tunanin (Obaseki) ya mutu murus a siyasance, mutane sun yanke Monday wanda suka zaɓa ya zama sanata bara, shi suke so kuma ga shi ya zama zaɓaɓɓen gwamna."

Kara karanta wannan

'An yi kwacen mulki a Edo,' Gwamna ya yi zazzafan martani kan zabe

Dalilan da suka ba APC nasara a Edo

A wani rahoton kun ji cewa masu hasashe sun fara fitar da dalilai kan abubuwan da suka sa dan takarar APC, Monday Okpebholo ya samu nasara a zaben.

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu abubuwa da ake hasashen su ne suka ba APC damar samun nasara kan PDP a zaɓen Edo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262