Abubuwa 5 da Suka Jawo APC Ta yi Nasara a Zaben Gwamnan Edo

Abubuwa 5 da Suka Jawo APC Ta yi Nasara a Zaben Gwamnan Edo

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da cewa jam'iyyar APC ce ta lashe zaben gwamna a Edo da ya gudana a ranar Asabar
  • Masu hasashe sun fara fitar da dalilai kan abubuwan da suka sa dan takarar APC, Monday Okpebholo ya samu nasara a zaben
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu abubuwa da ake hasashen su ne suka ba APC damar samun nasara kan PDP a zaɓen Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da cewa dan takarar APC, Monday Okpebholo ne ya lashe zaben gwamna a Edo.

Hakan na zuwa ne bayan an fafata sosai tsakanin Monday Okpebholo da Asue Ighodalo na jami'yyar PDP a zaɓen.

Kara karanta wannan

Baki har kunne: Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya samu manyan nasarori a cikin mako 1

Zaben Edo
Abubuwan da suka sa APC ta yi nasara a zaben Edo. Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Mun tattaro muku wasu abubuwa da ake ganin su ne suka ba Monday Okpebholo nasara a kan sauran yan takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da suka ba APC nasara a zaben Edo

1. Sabani da Oba na Benin

Rahoton Jaridar Daily Trust ya nuna cewa akwai sabani a tsakanin Oba na Benin da gwamna Godwin Obaseki wanda hakan ya yi tasiri sosai wajen kayar da PDP a zaɓen.

Rahotanni sun nuna cewa sabanin har ya kai ga shiga kotu ta bayan fage tsakanin bangaren gwamna da fada.

2. Ramuwar Adams Oshiomhole

Adams Oshiomhole ya kasance tsohon mai gida ga gwamna Godwin Obaseki amma suka fara jan daga har Obaseki ya koma PDP ya bar Oshimole a APC.

Oshiomhole ya kasance gawurtaccen dan siyasa kuma mai son ganin ya kayar da jam'iyyar Obaseki domin ya nuna masa cewa shi yaro ne man kaza.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 game da sabon gwamnan Edo, Okpebholo da aka zaba

3. Rikici da tsige Philip Shaibu

Philip Shaibu ya kasance mataimakin gwamnan jihar Edo amma sun samu samu da gwamna Obaseki wanda har suka raba jam'iyya.

Legit ta ruwaito cewa Philip Shaibu ya ce sun kai su 600 da suka fice daga PDP zuwa APC domin yiwa PDP illa a zaben Edo na 2024.

4. Edo ba Legas ba ce

A zaben Edo na 2020, gwamna Obaseki ya yi amfani da taken cewa Edo ba Legas ba ce wajen kayar da APC.

A wannan karon kuma, dan takarar PDP ya shafe mafi yawan rayuwarsa a Legas ne wanda hakan ya jawo masa rashin karɓuwa sosai inda wasu ke ce masa: Edo ba Legas ba ce.

5. Ƙarfin gwamnatin tarayya

Gwamna Obaseki ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da karfi wajen kwace mulki a jihar Edo, duk da cewa jami'an tsaro sun ce ba za su nuna wariya ba.

Kara karanta wannan

"Ba a yi mana adalci ba:" Jam'iyyar LP ta fadi wanda ya ci zaben Edo

Wasu na ganin tura jami'an tsaro sosai Edo a lokacin zabe na cikin karfin da gwamnatin tarayya ta yi amfani da shi.

Yiaga ta ce akwai magudi a zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin sa-kai masu lura da yadda zaben gwamnan jihar Edo da ya gudana a ranar Asabar sun fara fitar da rahoton bayan zabe.

Yiaga Africa ta fitar da rahoto kan yadda zaben ya gudana da kuma kura-kurai da ta ce an tafka a ɓangaren hukumar INEC ta kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng