Muhimman Abubuwa 5 game da Sabon Gwamnan Edo, Okpebholo da Aka Zaba

Muhimman Abubuwa 5 game da Sabon Gwamnan Edo, Okpebholo da Aka Zaba

An gudanar da zaben gwamnan jihar Edo a ranar Asabar 21 ga watan Satumbar 2024 yayin da Gwamna Obaseki ke shirin kammala wa'adinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Abubuwa muhimman game da sabon zababben gwamnan Edo
Hukumar INEC ta sanar da Monday Okpebholo na APC a matsayin wanda ya lashe zaben Edo. Hoto: Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Okpebholo ya samu kuri'u 291,667 yayin da dan takarar PDP, Asue Ighodalo ya samu kuri'u 247,274 a zaben, cewar rahoton Tribune.

Legit Hausa ta jero muku muhimman abubuwa game da Okpebholo wanda ya lashe zaben:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Shekaru da Ilimi

An haifi Monday Okebholo a shekarar 1970 wanda yanzu haka yana da shekaru 54 kenan.

Kara karanta wannan

'Dan PDP ya fashe da kuka a bidiyo yayin hira a gidan talabijin kan zabe

Okpebholo ya fara a karatu a Uromi kafin ya shiga Jami'ar Benin inda ya karanta bangaren harkokin noma kafin komawa karatu ya samu digiri na gaba.

2. Iyalai da taimako

Ubagiji ya albarkaci Monday Okpebholo da iyalai inda ya yi aure da mata kuma yana da yara guda hudu.

Okpebholo yana da gidauniya da yake taimakawa al'umma ta bangaren tallafin karatu da harkokin lafiya da koyon sana'o'i.

3. Siyasa da kasuwanci

Sabon zababben gwamnan ya kasance babban dan kasuwa da ya kware a bangaren gine-gine da noma da kuma harkokin mai.

Okpebholo ya fara siyasa tun 2003 inda aka zabe shi a matsayin dan Majalisar Wakilai a Najeriya karkashin jam'iyyar PDP.

4. Addini

Monday Okpebholo ya kasance mai son addini matuka wanda ya kasance cikakken mamba a cocin Redeemed Christian Chiruch of God (RCCG).

5. Kamfe

Yayin da ake yakin neman zaben gwamnan jihar Edo, Okpebholo ya sha alwashin tabbatar da gudanar da gwamnati ta kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya dura kan gwamna, ya ce ya mutu murus a siyasar Najeriya

Okpebholo ya yi alkawarin mayar da hankali wurin tattalin arziki da tallafi domin gina rayuwar matasa.

Zababben gwamnan Edo ya sha alwashi

Kun ji cewa zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya dauki alkawarin cicciba jihar zuwa matakin da kowa zai yi alfahari.

Mista Okpebholo ya dauki alkawarin daukar tsarin mulki irin na tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomole.

Ya godewa jama'ar da suka fito tare da ba shi kuri'a 291,667 wanda ya ba shi damar lallasa takwarorinsa na PDP da LP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.