An Karɓe Mulkin Edo, Ganduje Ya Jero Jihohin da APC Za Ta Ƙwace Nan Gaba

An Karɓe Mulkin Edo, Ganduje Ya Jero Jihohin da APC Za Ta Ƙwace Nan Gaba

  • Abdullahi Umar Ganduje ya ce APC za ta kwafi dabarun da ta yi amfani da su a Edo wajen karɓe mulkin wasu jihohi a Kudu maso Gabas
  • Shugaban APC ya bayyana haka ne a wurin murnar nasarar da Sanata Monday Okpebholo ya samu a zaben gwamnan Edo na ranar Asabar
  • Ganduje ya ce kamata ya yi babbar jam'iyya kamar APC ta ja ragamar shiyyar Kudu maso Gabas, inda ya ce aikin da zai sa a gaba kenan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam'iyyar za ta yi amfani da dabrun Edo a zaben gwamnan jihar Ondo mai zuwa.

Kara karanta wannan

'PDP ta lashe zaben Edo,' Gwamna ya ɓaro zancen da ya saɓa hukuncin INEC

Abdullahi Ganduje ya ƙara da cewa APC za ta ci gaba da amfanin waɗannan dabaru da suka ba ta nasara a Edo wajen ƙwace mulkin jihar Anambra da wasu jihohin Kudu maso Gabas.

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Shugaban APC ya lashi takobin kwato wasu jihohi bayan nasarar Edo Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Ganduje ya yi murna da nasarar APC a Edo

Ya faɗi haka ne ranar Litinin a Abuja a wurin bikin murnar nasarar da Sanata Monday Okpebolo ya samu a zaben da aka yi ranar Asabar inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Kano ya ce kamata ya yi babbar jam'iyya kamar APC ta zama ita ke jan ragamar shiyyar Kudu masu Gabashin Najeriya ta fuskar siyasa.

Haka nan kuma Ganduje ya buƙaci jagororin jam'iyyar su tashi tsaye, su duƙufa aiki babu kama hannun yaro domin cika muradai da manufofin APC a kowane mataki.

APC na shirin ƙwace jihohin Kudu

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Manyan jiga jigai 5 da suka yaƙi gwamna, suka kayar da ɗan takarar PDP

A ruwayar jaridar Leadership, shugaban APC ya ce:

"Mun duƙufa aikin faɗaɗa waɗannan dabarun domin karɓe ƙarin jihohi. Baɗi jihar Anambra za ta biyo baya, ina ƙara tuna maku muna da aikin da muka sa a gaba.
"Za mu cire Kudu maso Gabas daga zargin wariya, wannan aiki yana da wahala amma ya zama tilas mu yi shi, zamu tunkari jihohi biyar na Kudu maso Gabas da ƙarfinmu.
"Yanzu dai muna da jihohi biyu amma sun mana kaɗan saboda haka za mu tunkari waɗannan jihohin da zummar karɓe wasu daga ciki."

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo

A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP ta ƙasa ta bayyana matsayarta game da nasarar da APC ta samu a zaɓen gwamnan jihar Edo da aka yi.

Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum ya yi fatali da sakamakon da INEC ta sanar, ya ce Ighodalo ne sahihin wanda ya ci zaɓe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262