Bayan Lallasa PDP a Edo, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Samun Gagarumar Nasara a Arewa
- Hukumar zaɓen jihar Sakkwato ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi ranar Asabar da ta gabata
- Shugaban hukumar, Alhaji Aliyu Suleiman ya bayyana ƴan takarar APC a mtsayin waɗanda suka lashe kujerun ciyamomi 23 da kansiloli
- Ana sa ran Mai girma Gwamna Ahmed Aliyu zai rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin kananan hukumomi da kansilolin a yau Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Jam'iyyar APC mai mulki ta samu nasarar lashe zaɓen kananan hukumomi 23 da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a jihar Sakkwato.
Shugaban hukumar zaɓen Sakkwato mai zaman kanta, Alhaji Aliyu Suleiman shi ne ya sanar da hakan ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, 2024.
APC ta samu gagarumar nasara a Sokoto
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Alhaji Aliyu ya ce APC ta lashe zaɓen ciyamomi 23 da dukkan kujerun kansiloli da ke faɗin gundumomin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar zaɓen ya kara da cewa jam'iyyun siyasa 15 ne suka shiga zaɓen suka fafafata da juna, wanda a ƙarshe ƴan takarar APC suka yi galaba.
PDP ta ki shiga zaben jihar Sokoto
Sai dai babbar jam’iyyar adawa a jihar, PDP ba ta shiga zaben ba saboda abin da ta kira rashin adalci da kuma shirin yin maguɗi.
Idan ba ku manta ba, Gwamma Ahmed Aliyu ya roƙi jam'iyyar PDP da ta sake tunani, ta dawo ta shiga a fafata da ita a zaben.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a wurin kamfen jam'iyyar APC, inda ya ce gwamnatinsa ta shirya gudanar da sahihin zaɓe da kowa zai yi na'am da shi.
Gwamna Aliyu zai rantsar da ciyamomi
Jim kaɗan bayan sanar da waɗanda suka samu nasara, hukumar zaɓen ta ba su takardar shaidar zama zaɓaɓɓun ciyamomi da kansiloli.
Bayanai sun nuna cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya shirya rantsar da waɗanda suka samu nasara yau Litinin da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a cewar Tribune Nigeria.
Gwamnan Sokoto ya caccaki PDP
Ku na da labarin gwamnatin jihar Sakkwato ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yada karya kan ayyukan da ta ke yi wa jama'a.
Gwamna Ahmed Aliyu ya zargi PDP da daukar nauyin yada labaran karya kan kwangilar shingen titunan jihar da gwamnatinsa ta yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng