"Ba Mu Yarda ba," Shugaban PDP na Ƙasa Ya Faɗi Matakin da Za Su Ɗauka kan Zaɓen Edo

"Ba Mu Yarda ba," Shugaban PDP na Ƙasa Ya Faɗi Matakin da Za Su Ɗauka kan Zaɓen Edo

  • Jam'iyyar PDP ta ƙasa ta bayyana matsayarta game da nasarar da APC ta samu a zaɓen gwamnan jihar Edo da aka yi ranar Asabar
  • Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum ya yi fatali da sakamakon da INEC ta sanar, ya ce su ne wadanda suka ci zaɓe
  • Damagum ya ce za su garzaya gaban alƙali domin ƙwato haƙƙin ɗan takararsu da aka ƙwace, ya ƙara da cewa daman sun yi tunanin haka za ta faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jam'iyyar PDP ta yi fatali da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo wanda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta sanar.

Jam'iyyar PDP ta ƙasa ta ce ba ta yarda da sakamakon zaben da INEC ta sanar ba bayan kammala tattara alƙaluman ƙuri'un da aka kaɗa ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Manyan jiga jigai 5 da suka yaƙi gwamna, suka kayar da ɗan takarar PDP

Shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum.
PDP ta yi fatali da sakamakon zaben Edo, ta lashi takobin ƙwato hakkinta a kotu Hoto: @OfficialPDP
Asali: Twitter

Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya yi a Abuja yau Litinin, Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu muka ci zaɓe" - Jam'iyyar PDP

Ambasada Damagum ya ƙara da cewa al'ummar jihar Edo sun fito kwansu da ƙwarƙwata sun zaɓi ɗan takarar PDP, Dr. Asue Ighodalo kuma shi suke son su ji an sanar ya ci zaɓe.

Ya buƙaci hukumar INEC ta yi amfani da sauran lokacin da ya rage mata bisa tanadin dokar zaɓe wajen gyara kura-kuran da ta tafka.

A cewar Damagum, tun farko PDP ta ja hankalin ƴan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki kan shirin APC na maguɗin zaben ranar Asabar.

Damagum ya ce dama PDP ta yi zargin APC ta haɗa kai da INEC da mataimakin sufetan ƴan sanda domin ƙwace Edo da ƙarfi da yaji.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Ana jiran karamar hukuma 1, APC ta ba PDP tazarar kuri'u sama da 50,000

PDP ta shirya kai ƙara kotu

Shugaban rikon PDP ya ce:

“Duk da tashin hankali, tsoratarwa da magudin APC, sakamakon da aka samu daga rumfunan zabe ya nuna ɗan takararmu, Asue Ighodalo ne ya ci zaɓe kafin a sauya alƙaluman a ɗakin tattara sakamako.

Damagum.ya ce duk da haka jam'iyyar za ta sake gwada sashen shari'ar ƙasar nan domin ganin iya adalcin da za a masu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

APC ta shirya karɓo wasu jihohin kudu

A wani rahoton kuma Abdullahi Umar Ganduje ya ce APC za ta kwafi dabarun da ta yi amfani da su a Edo wajen karɓe mulkin wasu jihohi a Kudu maso Gabas

Shugaban APC ya bayyana haka ne a wurin murnar nasarar da Sanata Monday Okpebholo ya samu a zaben gwamnan Edo na ranar Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262