"Ba a Yi Mana Adalci Ba:" Jam'iyyar LP Ta Fadi Wanda Ya Ci Zaben Edo
- Jam'iyyar LP ta bayyana cewa dan takararta, Barista Olumide Akpata ne mutanen jihar Edo su ka zaba a zaben da ya gabata
- A ranar Asabar ne hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta gudanar da zaben gwamnan Edo a kananan hukumomi 18
- Bayan tattara sakamakon zaben a ranar Lahadi, hukumar INEC ta bayyana dan takarar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Edo - Shugaban LP reshen jihar Edo, Kelly Ogbalo ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben da dan APC ya yi nasara.
Hon. Kelly Ogbalo ya yi zargin hukumar zaben kasar nan (INEC) ta bari an yi amfani da ita wajen tafka magudin zaben da dan takarar LP ya zo na uku.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa daga cikin dokokin gudanar da sahihin zabe da LP ta yi zargin an karya akwai sayen kuri'a, kuma a bainar jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben Edo: LP ta ga gazawar jami'an tsaro
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa LP ta zargi jami'an tsaro da gaza taka birki kan masu tallar jam'iyyu da sayen kuri'a a rumfunan zaben da ya gudana a jihar Edo.
LP na ganin da an tabbatar da gudanar da sahihin zabe, babu abin da zai hana dan takararta, Olumide Akpata zama zaɓaɓɓen gwamnan jihar.
Jam'iyyar LP na ganin ita ta ci zaben Edo
Shugaban LP, Kelly Ogbalo ya bayyana yakinin cewa jam'iyyarsa ce ta yi nasara a zaben mutanen Edo su ka zabi sabon gwamna na wa'adin shekara hudu.
Hon. Ogbalo ya yi takaicin yadda ya ce an murde zaben tare da tafka rashin gaskiya bayan hukumar INEC ta ce dan takararta ya samu kuri'a 22,763.
Zaben Edo: PDP ta zargi INEC da magudi
A baya kun ji yadda jami'yyar PDP reshen jihar Ondo ta bayyana dan takararta Monday Okpebhola a matsayin zabin al'ummar jihar Edo, amma aka yi murdiya da rashin adalci.
PDP ta zargi INEC da hada kai da jam'iyyar APC wajen hana mutanen Edo zabinsu, tare da bayyana hakan a matsayin yi wa dimokuradiyyar kasar nan karan tsaye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng