‘Mu Muka Jawo,’ Mataimakin Gwamnan Edo Ya Tono Sirrin Faduwar PDP a Zaɓe

‘Mu Muka Jawo,’ Mataimakin Gwamnan Edo Ya Tono Sirrin Faduwar PDP a Zaɓe

  • Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu ya fadi wasu abubuwan da suka tattauna da gwamna Godwin Obaseki kafin zaben 2024
  • Philip Shaibu ya ce wasu maganganu da gwamna Obaseki ya fada musu ne suka fusata wasu daga cikinsu kuma hakan ya yi tasiri a zaben
  • Har ila yau mataimakin gwamnan ya fadi yadda Adams Oshimole ya kawo gwamna Godwin Obaseki kan kujerar gwamnan jihar Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya yi magana kan abin da ya saka PDP faduwa a zaben gwamna a Edo.

Philip Shaibu ya kuma yi karin haske kan dalilin da ya saka shi ficewa daga PDP zuwa jami'yyar APC.

Kara karanta wannan

'PDP ta lashe zaben Edo,' Gwamna ya ɓaro zancen da ya saɓa hukuncin INEC

Philip Shaibu
Mataimakin gwamna ya fadi yadda suka kayar da PDP a Edo. Hoto: Philip Shaibu
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta wallafa bidiyo a Facebook mataimakin gwamnan na cewa gwamna Godwin Obaseki ya fada musu maganganu marasa dadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene ya jawo faduwar PDP a zaben Edo?

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya ce PDP ta fadi ne saboda Godwin Obaseki ya yi fada da jiga jigan yan siyasa da suka mara masa baya.

Philip Shaibu ya ce daɗin daɗawa gwamna Obaseki ya ce ga mutane tara da suka yi takarar fitar da gwani a PDP ko da su ko ba su zai yi nasara a zabe.

Haka zalika ya ce kusan kusoshin PDP 600 suka fice zuwa APC tare da shi saboda halin gwamnan wanda hakan na cikin abubuwan da suka kayar da PDP a zaɓen Edo.

Yadda Obaseki ya zama gwamna a Edo

Philip Shaibu ya ce su ne suka taimakawa gwamna Godwin Obaseki har ya zama gwamna a jihar Edo.

Kara karanta wannan

"Za a sharbi romon dimukuradiyya:" Zababben gwamnan Edo ya yi albishir

Mataimakin gwamnan ya ce tsohon gwamnan jihar, Adams Oshimole ne ya ce su goya masa baya su kuma suka amsa kiran a lokacin.

Shaibu ya kuma yi ikirarin cewa ko a lokacin da gwamna Godwin Obaseki ya nemi takara karo na biyu su suka masa tsayuwar daka.

Obaseki ya yi korafi kan zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya nuna takaici kan yadda hukumar INEC ta sanar da APC ta lashe zaben gwamna.

Godwin Obaseki ya yi kira na musamman ga al'ummar jihar Edo kan cigaba da rungumar zaman lafiya duk da abin da ya faru a zaben Edo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng