"INEC ba Ta Mutunta Zabin Mutanen Edo ba:" PDP Ta Ce An Ci Mutuncin Dimukuradiyya

"INEC ba Ta Mutunta Zabin Mutanen Edo ba:" PDP Ta Ce An Ci Mutuncin Dimukuradiyya

  • Jam'iyyar PDP ta zargi hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da APC da yi wa dimukuradiyya karan tsaye a zaben jihar Edo
  • PDP ta reshen jihar Ondo ta yi zargin cewa INEC da APC sun san sahihin zababben gwamna a jihar, amma su ka yi gaban kansu
  • Mashawarci na musamman na yakin neman zaben PDP a jihar, Ayo Fadaka ya ce an yi laifi wajen ba Monday Okpebhola nasara a Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ta bi sahun uwar jam'iyyar wajen watsi da sakamakon zaben gwamnan Edo da APC nasara.

Kara karanta wannan

'PDP ta lashe zaben Edo,' Gwamna ya ɓaro zancen da ya saɓa hukuncin INEC

Hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa APC ta samu kuri'a 291,667 yayin da PDP ta samu kuri'a 247,274 bayan tattara sakamon zaben.

Zaben
PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Edo Hoto: Asue Ighodalo - AI Comms
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mashawarci na musamman na yakin neman zaben PDP a jihar, Ayo Fadaka ya ce sam babu adalci a sakamakon zaben Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP ta zargi INEC, APC da magudi

Jam'iyyar PDP ta zargi hukumar zabe ta kasa (INEC) da yi wa dimukuradiyya karan tsaye wajen bayyana Monday Okpebhola a matsayin gwamna.

Ayo Fadaka, mashawarci na musamman na yakin neman zaben PDP a Ondo ya ce hukumar zabe da APC ba ta mutunta abin da jama'ar Edo su ka zaba ba.

PDP ta ce INEC ta take doka a zaben Edo

PDP a jihar Ondo ta ce hukumar INEC ta san cewa APC ba ta ci zaben gwamnan Edo da aka gudanar a ranar Asabar ba.

Kara karanta wannan

"Za a sharbi romon dimukuradiyya:" Zababben gwamnan Edo ya yi albishir

Jam'iyyar da ke mulki a Edo ta kara da cewa INEC ta yi abin kunya wajen take doka da cin amanar mutanen Edo wajen bayyana APC a matsayin mai nasara.

Zababben gwamna ya godewa mutanen Edo

A baya mun ruwaito cewa zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebhola ya gode wa jama'ar da su ka zabe shi a ranar Asabar, tare da daukar alkawarin kawo ayyukan ci gaba.

Sanata Monday Okpebhola ya bayyana cewa zai dauki salon mulkin tsohon gwamna Adams Oshiomhole na jihar da na Sanata Godswill Akpabio.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.