‘PDP Ta Lashe Zaben Edo,’ Gwamna Ya Ɓaro Zancen da Ya Saɓa Hukuncin INEC

‘PDP Ta Lashe Zaben Edo,’ Gwamna Ya Ɓaro Zancen da Ya Saɓa Hukuncin INEC

  • Gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri ya yi karin haske kan maganar da ya yi ta cewa jam'iyyar PDP ce ta lashe zabe a jihar Edo
  • Umaru Fintiri ya zargi shugaban jam'iyyar APC na kasa da wasu jiga jigan jami'yyar da karya doka a ranar zaben gwamna a Edo
  • Haka zalika Umaru Fintiri ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta da rashin yi wa jam'iyyar PDP adalci a harkar zaben baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yi magana da ta tayar da kura kan zaben gwamna a jihar Edo.

Umaru Fintiri ya zargi hukumar INEC da goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki a yayin zaben da ya gabata a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

"INEC ba ta mutunta zabin mutanen Edo ba:" PDP ta ce an ci mutuncin dimukuradiyya

Umaru Fintiri
Gwamna Fintiri ya ce ba a yi adalci a zaben Edo ba. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanan da Gwamna Umaru Fintiri ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fintiri ya ce PDP ce ta ci zaɓe a Edo?

Gwamna Umaru Fintiri ya ce APC ta zarge shi da cewa ya ce PDP ce ta lashe zaben Edo duk da cewa hakan gaskiya ne.

Fintiri ya ce idan aka lura da kuri'un da APC da PDP suka samu a shafin IREV na INEC za a tabbatar da cewa PDP ce a gaba yayin zaben.

Fintiri ya ce INEC ta goyi bayan APC

Gwamna Umaru Fintiri ya ce hukumar zabe ta nuna wariya ga jami'yyar PDP yayin zaben gwamna a jihar Edo.

Umaru Fintiri ya kara da cewa an samu masu sayen kuri'a, cusa kuri'un bogi da katsalandan wajen tattara kuri'u amma duk da haka INEC ta ba APC nasara maimakon ta yi bincike.

Kara karanta wannan

'An yi kwacen mulki a Edo,' Gwamna ya yi zazzafan martani kan zabe

Fintiri: 'Ganduje ya karya doka a zaben Edo'

Gwamnan jihar Adamawa ya zargi shugaban APC, Abdullahi Ganduje da karya dokar hana fita da yan sanda suka saka a Edo ranar zabe.

Ya ce Ganduje ya shiga jihar Edo a ranar zabe tare da wasu gwamnonin APC, kuma sun yi amfani da jami'an tsaro wajen yin barazana ga masu zabe.

Obaseki ya yi magana kan zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya nuna takaici kan yadda hukumar INEC ta sanar da APC ta lashe zaben gwamna.

Godwin Obaseki ya yi kira na musamman ga dukkan al'ummar jihar Edo kan cigaba da rungumar zaman lafiya duk da abin da ya faru a Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng