‘An yi Kwacen Mulki a Edo,’ Gwamna Ya yi Zazzafan Martani kan Zabe
- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya nuna takaici kan yadda hukumar INEC ta sanar da cewa APC ta lashe zaben gwamna
- Godwin Obaseki ya yi kira na musamman ga al'ummar jihar Edo kan cigaba da rungumar zaman lafiya duk da abin da ya faru a Edo
- A jiya Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da cewa dan takarar APC, Monday Okpebholo ne ya lashe zaben da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi kira na musamman ga al'ummar Edo bayan sanar da sakamakon zaben gwamna.
Godwin Obaseki ya bukaci a cigaba da zaman lafiya duk da cewa ya ce an tafka kurakurai a wajen tattara sakamakon zaɓen.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Godwin Obaseki ya ce tamkar an yi kwacen mulki a jihar ne wanda hakan ya saɓa tsarin dimokuraɗiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar kwacen mulki a zaben Edo
Gwamna Godwin Obaseki ya ce daɗin dimokuraɗiyya shi ne ta ba mutane damar zaben wanda suke so ya shugabance su.
Amma ya ce idan aka kwace mulki da karfin tsiya aka mikawa wanda bai cancanta ba, kamar yadda aka yi a Edo, an nakasa dimokuraɗiyya.
Gwamna ya ce a yi hakuri kan zaben Edo
Gwamna Godwin Obaseki ya yi kira ga al'ummar Edo kan yin hakuri wajen murdiya da ya ce an yi a zaben Edo na ranar Asabar.
Ya ce duk da an nunawa mutanen Edo karfi wajen kwace abin da suka zaba, ya kamata su yi hakuri saboda tabbatar da zaman lafiya.
An karya dokoki a zaben Edo inji Obaseki
Gwamna Godwin Obaseki ya ce a zahiri lamarin yake kan cewa an karya dokoki a zaben da ya gudana a Edo.
Business Day ta wallafa cewa Obaseki ya ce ya kamata waɗanda aka zalunta su nufi kotu domin kwato hakkokinsu da aka danne.
Talakawa sun amince da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana bayan jami'yyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Edo.
Sanata Barau Jibrin ya ce nasarar jami'yyar APC a zaɓen alama ce da ke nuna cewa talaka na goyon bayan tsare tsaren Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng