Zaben Edo: Manyan Jiga Jigai 5 da Suka Yaƙi Gwamna, Suka Kayar da Ɗan Takarar PDP

Zaben Edo: Manyan Jiga Jigai 5 da Suka Yaƙi Gwamna, Suka Kayar da Ɗan Takarar PDP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Edo - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ranar Asabar.

Baturen zaɓen wanda shi ne shugaban jami’ar fasaha ta tarayya da ke Minna, Farfesa Faruk Adamu Kuta, ya ce dan takarar APC, Sanata Monday Okpebolo ya samu kuri’u 291,667.

Asue Ighodalo.
Manyan ƴan siyasa da suka yaki Obaseki da PDP a zaben gwamnan Edo Hoto: Asue Ighodalo
Asali: Twitter

Hakan ya ba shi damar lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP Asue Ighodalo wanda ya samu kuri'u 247,274, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Legit Hausa ta tattaro muku manyan jiga-jigai biyar waɗanda suka taka rawa wajen kayar da PDP a zaɓen Edo saboda saɓaninsu da Gwamna Godwin Obaseki.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin gwamna na shirin sauya sheƙa, ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ministan Abuja, Nyesom Wike

A lokacin da APC ta hana Obaseki tikitin neman tazarce a zaɓen gwamnan Edo na 2020, Nyesom Wike da wasu ƙusoshin PDP sun taka rawa wajen ba shi tikitin jam'iyyar.

Wike, wanda a lokacin yana matsayin gwamnan Ribas, ya marawa Gwamna Obaseki baya har ya samu nasarar lallasa ɗan takarar APC Osagie Ize-Iyamu a zaɓen 2020.

Ba a daɗe ba bayan ya samu nasara, Obaseki ya fara takun saƙa da Wike, a taƙaice ma gwamnan ya goyi bayan takarar Atiku Abubakar maimakon Wike a 2023.

Daga baya Wike ya nemi afuwar Sanata Adams Oshiomhole, tsohon ubangidan Obaseki saboda "taimakawa Gwamna Obaseki ya yi tazarce."

Gabanin zaɓen ranar Asabar, Wike wanda a yanzu yake kujerar ministan Abuja ya ce ba zai goyi bayan dan PDP, Asue Ighodalo ba saboda alaƙarsa da Obaseki ta yi tsami.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya dura kan gwamna, ya ce ya mutu murus a siyasar Najeriya

Sai dai a wata hira da aka yi da shi, Obaseki ya ce mutanen jihar Edo ba su bukatar goyon bayan Wike kafin su yanke wanda za su damkawa amanar jiharsu.

2. Kwamared Philip Shaibu

A lokacin da rigima ta yi zafi tsakanin Obaseki da Oshiomhole musamman a 2020, Kwamared Philip Shaibu ya zaɓi zama a tsagin Gwamna Obaseki.

Kamar dai Wike, Shaibu ya taka rawa wajen tabbatar da sake zaben Obaseki. Shi ne ya tunkari Oshiomhole har inda yake taƙama da shi, ya rika jifansa da kalamai mara daɗi.

Sai dai reshe ya juye da Shaibu bayan ya nuna sha'awar neman takarar gwamna domin bayan hana shi tikitin takara, Gwamna Obaseki ya kitsa tsige mataimakin gwamnan.

A watan Yuli, babbar kotun tarayya ta maido Shaibu kan kujerar mataimakin gwamna kuma bayan haka ya jagoranci manyan ƙusoshin PDP suka haɗe da APC.

Sauya sheƙar Shaibu ta naƙasa PDP a lokacin da ake tunkarar zaɓen gwamna wanda aka yi ranar Asabar, 21 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Yadda APC ta lashe zabe bayan samun nasara a kananan hukumomi 11

3. Dan Orbih

Tsohon mataimakin shugaban PDP na Kudu maso Kudu kuma tsohon shugaban jam'iyyar a Edo, Dan Oribih na ɗaya daga cikin manyan ƙusoshin da suka kayar da Ighodalo.

Lokacin da Ighodalo ya zama dan takarar PDP, Dan Orbih wanda yana ɗaya daga cikin ƴan tsagin Wike ya bayyana cewa ba zai mara masa baya ba.

Hasali ma, ya ƙi amince da tayin shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP, inda ya ce babu wanda ya nemi shawararsa ƙafin sanya sunansa a kwamitin kamfe.

"Wasu mutane da suka ga sunana ne suka kirani suka gaya mun, ni ban ma sani ba kuma ba na cikin waɗanda suka tsara tawagar kamfen," in ji Orbih.

4. Anslem Ojezua

Mista Ojezua na ɗaya daga cikin makusantan Obaseki a siyasa waɗanda suka rikiɗe suka zama abokan faɗa.

Anslem Ojezuwa shi ne shugaban APC na Edo wanda ya jagoranci manyan ƙusoshi zuwa PDP lokacin da aka hana Gwamna Obaseki tikitin tazarce a 2020.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Gwamna ya sha kaye a karamar hukumarsa, APC ta yi nasara

Kamar Shaibu, alaƙar Ojezua da Obaseki ta yi tsami ne lokacin da ya nuna sha'awar takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP.

Bayan mutumin Obaseki ya samu nasarar zama dan takarar PDP, Ojezua ya caccaki zaben fidda gwanin kuma ya maka Ighodalo a kotu.

5. Hon. Kabiru Adjoto

Shi ne tsohon kakakin majalisar dokokin Edo wanda ya fice daga jam’iyyar PDP bayan ya samu sabani da Gwamna Obaseki. 

Ana raɗe-raɗin Kabiru Adjoto ya samu saɓani da Gwamma Obaseki ne sakamakon ƙin naɗa shi a matsayin mataimakin gwamna bayan tsige Shaibu.

Godwin Obaseki ya bayyana Marvelous Omobayo a matsayin mataimakinsa, lamarin da aka ce ya fusata Adjoto.

Obaseki ya roƙi mutane su zauna lafiya

A wani rahoton kuma gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya nuna takaici kan yadda INEC ta sanar da cewa APC ta lashe zaben gwamna.

Godwin Obaseki ya yi kira na musamman ga al'ummar jihar Edo kan cigaba da rungumar zaman lafiya duk da abin da ya faru a Edo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262