Edo 2024: Yadda APC Ta Lashe Zabe bayan Samun Nasara a Kananan Hukumomi 11

Edo 2024: Yadda APC Ta Lashe Zabe bayan Samun Nasara a Kananan Hukumomi 11

  • Dan takarar jam'iyyar APC, Monday Okpebholo ya lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar 21 ga watan Satumba
  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Okpebholo matsayin wanda ya lashe zaben bayan samun kuri'u 291,667
  • Legit Hausa ta tattaro cewa jam'iyyar APC ta samu nasara a kananan hukumomi 11 yayin da mai bi mata, PDP ta samu lashe guda bakwai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo.

A ranar Asabar, 21 ga watan Satumba ne aka gudanar da zaben inda INEC ta sanar da sakamakon a ranar Lahadi a birnin Benin.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Jerin kananan hukumomin da Ighodalo na PDP ya lashe

Jam'iyyar APC ta samu nasara a kananan hukumomi 11 cikin 18 na jihar Edo
Edo 2024: Dan takarar APC, Monday Okpebholo ya lashe zabe a kananan hukumomi 11. Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Twitter

Legit Hausa ta ruwaito cewa Monday Okpebholo ya lashe zaben Edo ne da kuri'u 291,667 bayan da ya samu nasara a kananan hukumomi 12 cikin 18 na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon zaben jihar Edo

Duk da cewa jam'iyyar PDP ce ke mulki a Edo, sai dai hakan bai hana al'umma zaben wanda suke ganin shi ne ya fi cancanta ya gaji Gwamna Godwin Obaseki ba.

Amma dai jam'iyyar PDP ta nuna rashin amincewarta kan wannan sakamako inda ta yi ikirarin cewa an tafka kurarai musamman a wajen tattara sakamako.

A jimillar kananan hukumomi 18 na Edo, APC ta samu kuri'u 291,667 yayin da PDP ta zo ta biyu da kuri'u 247,655 inda LP ke da kuri'u 22,763.

Kananan hukumomin da APC ta lashe

Ga jerin kananan hukumomin da dan takarar APC, Monday Okpebholo ya lashe a zaben, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Gwamnonin PDP sun ji wuta, sun tura sako ga INEC, sun soki Tinubu

1. Esan ta Yamma

APC - 12,952

PDP - 11,004

LP - 342

2. Owan ta Yamma

APC - 12,277

PDP - 11,284

LP - 201

3. Karamar hukumar Egor

APC - 16,760

PDP - 14,658

LP - 1,966

4. Akoko Edo

APC - 34,847

PDP - 15,865

LP - 2,239

5. Esan ta tsakiya

APC - 10,990

PDP - 8,618

LP - 418

6. Karamar hukumar Orhionmwon

APC - 16,059

PDP - 14,614

APC - 556

7. Owan ta Gabas

APC - 19,380

PDP - 14,189

LP - 446

8. Etsako ta Gabas

APC - 20,167

PDP - 9,683

LP - 604

9. Etsako ta tsakiya

APC - 11,906

PDP - 8,455

LP - 381

10. Etsako ta Yamma

APC - 32,107

PDP - 17,483

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Gwamna ya sha kaye a karamar hukumarsa, APC ta yi nasara

LP - 2,116

11. Karamar hukumar Oredo

APC - 30,780

PDP - 24,938

LP - 5,389

Edo: PDP ta lashe kananan hukumomi 7

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta samu nasarar lashe kananan hukumomi bakwai cikin 18 a zaben jihar Edo da aka gudanar.

Dan takarar PDP, Asu Ighodalo ya samu kuri'u 247,655 a dukkanin kananan hukumomin jihar yayin da Monday Okpebholo na APC ya lashe zaben da kuri'u 291,667.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.