Sakamakon Zaben Edo: Jerin Kananan Hukumomin da Ighodalo na PDP Ya Lashe

Sakamakon Zaben Edo: Jerin Kananan Hukumomin da Ighodalo na PDP Ya Lashe

  • Bayan kammala bayyana sakamakon zaben jihar Edo da hukumar INEC ta yi, an gano cewa jam'iyyar PDP ta lashe kananan hukumomi bakwai
  • Dan takarar PDP a zaben gwamnan Edo, Asue Ighodalo ya samu jimillar kuri'u 247,655 a dukkanin kananan hukumomin jihar 18
  • Sai dai hukumar INEC ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC, Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben Edo da kuri'u 291,667

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kammala tattarawa tare da bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Edo.

A ranar Asabar, 21 ga watan Satumbar nan ne aka gudanar da zaben gwamnan jihar yayin da INEC ta ayyana wanda ya alashe zabena a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Yadda APC ta lashe zabe bayan samun nasara a kananan hukumomi 11

Dan takarar PDP a Edo, Asue Ighodalo ya sha kasa a zaben gwamnan jihar
PDP ta samu nasara a kananan hukumomi 6 cikin 18, ga cikakken sunayensu. Hoto: @Aighodalo
Asali: Twitter

Sakamakon zaben gwamnan Edo

Legit Hausa ta ruwaito cewa INEC ta ayyana Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben Edo, kuma shi ne zababben gwamnan jihar na gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta tsaya kan matsayarta duk da cewa an samu zarge-zarge daga jam'iyyun adawa musamman PDP na kura-kurai a zaben da kuma kin amincewa da sakamako.

A jimillar kananan hukumomi 18 na Edo, APC ta samu kuri'u 291,667 yayin da PDP ta zo ta biyu da kuri'u 247,655 inda LP ke da kuri'u 22,763.

Kananan hukumomin da PDP ta lashe

Ga jerin kananan hukumomin da dan takarar PDP, Asue Ighodalo ya lashe a zaben, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

1. Karamar hukumar Igueben

PDP - 8,470

APC - 5,907

LP - 494

2. Karamar hukumar Uhunmwonde

Kara karanta wannan

Edo 2024: Gwamnonin PDP sun ji wuta, sun tura sako ga INEC, sun soki Tinubu

PDP - 9,339

APC - 8,776

LP - 767

3. Ovia ta Arewa maso Gabas

PDP - 15,311

APC - 13,225

LP - 1,675

4. Esan ta Kudu maso Gabas

PDP - 14,199

APC - 8,398

LP - 98

5. Esan ta Arewa maso Gabas

PDP - 12,522

APC - 10,648

LP - 194

6. Ovia ta Kudu maso Yamma

PDP - 10,260

APC - 10,150

LP - 849

7. Karamar hukumar Ikpoba-Okha

PDP - 26,382

APC - 16,338

LP - 4,026

Duba wasu labarai a kan zaben Edo

Sakamakon zaben Edo: APC ta ba PDP tazarar sama da kuri'u 50,000

Zaben Edo: APC ta lashe kananan hukumomi 12, PDP ta tsira da 6

Gwamna Obaseki ya ba PDP kunya, APC ta lashe karamar hukumarsa

INEC ta yi barazanar soke zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi barazanar soke zaben gwamnan jihar Edo da aka dora a shafinta na IReV.

INEC ta ce ma damar ta gano cewa an tursasa wani jami'inta ayyana sakamakon zabe, ta ce za ta yi amfani da karfin ikonta wajen soke zaben wannan rumfa ko mazaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.