Edo 2024: Gwamnonin PDP Sun Ji Wuta, Sun Tura Sako ga INEC, Sun Soki Tinubu
- Yayin da ake jiran sakamakon zaben jihar Edo, gwamnonin PDP sun gargadi hukumar zabe kan sanar da sakamako na gaskiya
- Shugaban kungiyar gwamnonin, Bala Mohammed ya nuna damuwa kan halin da kasa ke ciki inda ya ka bukaci INEC ta yi adalci
- Gwamna Bala Mohammed ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da jam'iyyar APC a matsayin barazana ga dimukradiyyar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun tura sako ga hukumar zabe ta INEC a Najeriya.
Gwamnonin sun bukaci INEC ta mutunta zabin al'umma yayin da ake tattara sakamakon zaben jihar Edo.
Edo: Jam'iyyar PDP ta koka kan zabe
Shugaban kungiyar gwamnonin, Gwamna Bala Mohammed daga Bauchi shi ya bayyana haka a wata sanarwa da PDP ta wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Bala ya ce yayin da kasar ke fuskantar matsalolin rashin tsaro da matsin tattalin arziki, ya kamata INEC ta mutunta zabin al'umma.
"Muna fama da matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki, muna tsammanin INEC ta take gudanar da zaben Edo za ta mutunta zabin jama'a."
"Hakan zai dakile kasar shiga wani mummunan hali idan har aka tafka magudin zabe ko sanar da sakamakon da ba dai-dai ba."
"Wannan ya zama dole duba da barazana da dimukradiyya ke ciki na neman kwace jihohi da Gwamnatin Tinubu da APC ke yi."
- Sanata Bala Mohammed
Wannan na zuwa ne bayan dan takarar gwamnan a PDP, Asue Ighodalo ya nuna damuwa kan yadda jami'an tsaro suke cafke magoya bayan PDP.
Ighodalo ya koka kan yadda aka samu jinkirin samar da kayayyakin zabe a wuraren da ya fi karfi da al'umma.
Okpebholo na APC ya lashe zaben gwamnan Edo
Kun ji cewa bayan tattara sakamakon zaben jihar Edo, hukumar zabe ta INEC ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben.
Hukumar ta bayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jiya Asabar.
Wannan na zuwa ne bayan kada kuri'u a zaben da aka gudanar a jiya Asabar 21 ga watan Satumbar 2024 a Edo.
Asali: Legit.ng