Zaben Edo: Ana Jiran Karamar Hukuma 1, APC Ta ba PDP Tazarar Kuri'u Sama da 50,000
Edo - Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ranar Asabar, Sanata Monday Okpebholo, ya fara hangen nasara a zaben.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Asue Ighodalo ne ke biye da shi, yayin da Olumide Akpata na jam'iyyar Labour (LP), ya zo na uku.
Ya zuwa yanzu dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi 17, inji rahoton The Cable.
Legit Hausa ta ruwaito cewa dan takarar jam’iyyar APC ya lashe kananan hukumomi 11 cikin 17, wanda ya zuwa yanzu INEC ta tattara kuma ta bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sakamakon da aka bayyana kawo yanzu, Okpebholo ya samu kuri’u 275,329 yayin da Ighodalo ya samu kuri’u 220,892, inda ya bar tazarar kuri’u 54,437.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ikpoba-Okha ita ce karamar hukumar da ake jiran shigowar sakamakonta.
Karashen labarin na zuwa...
Asali: Legit.ng