Sakamakon Zaben Edo: Gwamna Ya Sha Kaye a Karamar Hukumarsa, APC Ta Yi Nasara
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana jam'iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zabe a karamar hukumar Oredo, jihar Edo
- INEC ta bayyana cewa APC ta samu kuri'u 30,780 a karamar hukumar Oredo a zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar
- Karamar hukumar Oredo dai nan ce Gwamna Godwin Obaseki ya fito, inda kuma ya gaza ba jam'iyyarsa ta PDP nasara a cikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - An bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna a karamar hukumar Oredo ta jihar Edo, inda Gwamna Godwin Obaseki ya fito.
Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana, Sanata Monday Okpebolo, dan takarar APC ya samu kuri’u 30,780 a karamar hukumar.
A yayin da APC ta yi nasara a karamar hukumar, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dan takarar PDP, Asue Ighodalo ya samu kuri’u 24,938.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Edo: Sakamakon zaben Oredo
Olumide Akpata na jam'iyyar Labour ya samu kuri'u 5,389.
A ƙasa akwai sakamakon da aka sanar a cibiyar tattara sakamako ta jihar da ke Benin.
Wadanda suka yi rijista -356242
Wadanda aka tantance -64802
Kuri'un da aka kada – 64042
APC – 30780
LP – 5389
PDP – 24938
APGA - 523
Duba wasu labarai a kan zaben Edo:
Edo 2024: Jami'an EFCC sun cafke masu sayen kuri'a ana tsaka da zabe
Sakamakon zaben Edo: APC ta lashe kananan hukumomi 10, PDP kuma 6
Zaben jihar Edo: Dan takarar PDP ya samu nasara a karamar hukumarsa
Akwai dalili: INEC ta yi barazanar soke zaben jihar Edo da aka dora a IReV
"Dalilin ziyartar ofishin INEC" - Obaseki
A wani labarin, mun ruwaito Gwamna Godwin Obaseki ya ce ya ziyarci cibiyar tattara sakamako ta INEC da ke a jihar ne domin ya samu bayanai game da yadda abubuwa ke tafiya.
Hakazalika gwamnan ya ce ya je ofishin hukumar zaben ne domin ganawa da baturen zaben jihar don jin dalilin hana wakilan PDP shiga cibiyar tattara sakamakon zaben jihar.
Asali: Legit.ng