Edo 2024: INEC Ta Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna, an Lissafa Kuri'u

Edo 2024: INEC Ta Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna, an Lissafa Kuri'u

  • Bayan tattara sakamakon zaben jihar Edo, hukumar zabe ta INEC ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben
  • Hukumar ta bayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jiya Asabar
  • Wannan na zuwa ne bayan kada kuri'u a zaben da aka gudanar a jiya Asabar 21 ga watan Satumbar 2024 a Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo.

Hukumar ta tabbatar da Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jiya Asabar.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Ana jiran karamar hukuma 1, APC ta ba PDP tazarar kuri'u sama da 50,000

INEC ta sanar da wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Edo
Hukumar INEC ta tabbatar da Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a Edo. Hoto: Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Edo: INEC ta fadi wanda ya lashe zabe

Baturen zabe a jihar, Farfesa Faruk Adama Kuta shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar gwamna a APC ya samu kuri'u har 291,667 yayin da mai bi masa daga jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 247,244.

Vanguard ta tabbatar da cewa dan takarar gwamna a jam'iyyar LP, Olumide Akpata ya zama na uku inda ya samu kuri'u 22,763.

"Mr. Okpebholo bayan cika ka'idojin doka, shi ya yi nasarar lashe zaben da aka gudanar."

- Farfesa Faruk Kuta

Yawan kananan hukumomi a jihar Edo

Jihar Edo ta kunchi kananan hukumomi 18 wanda aka raba su zuwa mazabu uku da suka hada da Edo ta Arewa da ta Kudu da kuma ta Tsakiya.

Tun asali, Edo ta Arewa ta kasance inda jam'iyyar APC ta fi karfi yayin da PDP ke rike da Edo da Kudu da ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Gwamna ya sha kaye a karamar hukumarsa, APC ta yi nasara

PDP ta yi zanga-zanga kan zaben Edo

Kun ji cewa magoya bayan jam'iyyar PDP sun fara zanga-zanga game da zaben gwamnan jiha da ake yi a Edo saboda matsaloli.

Jam'iyyar ta nuna damuwa tun farkon zaben kan yadda lamura ke tafiya ba tare da tsari ba inda ta yi fatali da sakamakon.

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar INEC ta sanar da sakamakon kananan hukumomi 10 daga cikin 16 da APC ke kan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.