Edo 2024: Zanga Zanga Ta Barke kan Sakamakon Zabe, an Samu Bayanai
- Magoya bayan jam'iyyar PDP sun fara zanga-zanga game da zaben gwamnan jiha da ake yi a Edo saboda matsaloli
- Jam'iyyar ta nuna damuwa tun farkon zaben kan yadda lamura ke tafiya ba tare da tsari ba inda ta yi fatali da sakamakon
- Wannan na zuwa ne bayan Hukumar INEC ta sanar da sakamakon kananan hukumomi 10 daga cikin 16 da APC ke kan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Yayin da ake cigaba da tattara sakamakon zaben jihar Edo, zanga-zanga ta barke kan zargin magudi.
Magoya bayan jam'iyyar PDP ne suka runtuma tituna domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda lamura ke tafiya a zaben.
PDP ta koka kan zaben jihar Edo
Channels TV ta wallafa wani rahoto a shafin X da ke nuna yan PDP sun durfafi ofishin INEC da ake tattara sakamakon zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magoya bayan PDP sun nuna damuwa game da matsaloli da aka samu tun farkon zaben har zuwa lokacin tattara sakamako.
Wannan na zuwa ne bayan INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 16 daga cikin 18, cewar rahoton Premium Times.
Jam'iyyar APC ta lashe kananan hukumomi 10 daga cikin 16 yayin da PDP ta tsira da gudan shida kacal.
Dan takarar PDP ya koka a Edo
Tun farko, dan takarar gwamnan a PDP, Asue Ighodalo ya nuna damuwa kan yadda jami'an tsaro suke cafke magoya bayan PDP.
Ighodalo ya koka kan yadda aka samu jinkirin samar da kayayyakin zabe a wuraren da ya fi karfi da al'umma.
Dan takarar ya zargi makarshiya aka yi domin kassara shi da kuma neman yin magudi a zaben da ake yi.
Edo: Gwamnonin APC sun fara murnar zabe
Kun ji cewa gwamnonin APC sun fara murna tun kafin sanar da sakamakon zaben jihar Edo a hukumance yayin da ake cigaba da tattarawa.
An gano gwamnonin jihohin APC sun dukufa da addu'o'i da kuma murna yayin da ake sako sakamakon zaben.
Wannan na zuwa ne bayan.PDP ta fara korafi kan yadda lamura ke gudana inda ta ce ba ta gamsu da su ba.
Asali: Legit.ng