Edo 2024: PDP Ta Hango Faduwa, Ta Yi Fatali da Sakamakon Zaben Gwamna

Edo 2024: PDP Ta Hango Faduwa, Ta Yi Fatali da Sakamakon Zaben Gwamna

  • Jam'iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben da su ka fito daga kananan hukumomi biyu a jihar
  • Jami'in PDP da ke ofishin INEC, Osagbovo Iyoha ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da hada kai da jam'iyyar APC
  • Ya ce akwai karamar hukumar da aka dauke kidaya kuri'a zuwa wani waje na daban, kuma aka ki yin kidayar a gaban yan jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Edo - Jam'iyyar PDP ta bayyana rashin gamsuwa da alkaluman da su ka fito daga kananan hukumomin Egor da Akoko Edo bayan hukumar INEC ta fadi sakamakon su.

Jam'iyyar adawa ta APC a jihar ce ta yi nasara a kananan hukumomin biyu da su ka jawo matsala, inda PDP ta yi zargin an yi rashin gaskiya.

Jihar Edo
APC ta yi watsi da sakamakon zabe Hoto: Asue Ighodalo - AI Comms
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Osagbovo Iyoha, jami'in PDP a ofishin INEC inda aka fadan sakamakon ya yi zargin magudi a yankunan da hadin bakin hukumar zabe.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Gwamna ya sha kaye a karamar hukumarsa, APC ta yi nasara

PDP ta yi zargin magudi a zaben Edo

Wakilin PDP ofishin INEC a Benin ya bayyana cewa hukumar ta hada baki da APC wajen yin magudin zabe a kananan hukumomi biyu. Ya bayyana cewa hukumar INEC ta tafi wani waje daban inda ta tattara sakamakon, maimakon a hedkwatar karamar hukuma. Mista Iyoha ya kara da cewa ko a wancan waje da aka tattara sakamakon, ba a bar wakilan PDP sun ga abin da ya wakana ko yadda aka lissafa kuri'ar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An sauya sakamakon Akoko-Edo," PDP

Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa jami'an INEC sun hada baki da APC wajen sauya sakamakon zaben karamar hukumar Akoko-Edo. Jam'iyyar ta ce zarginta ya biyo bayan yadda adadin wadanda su ka kada kuri'a ya fi wanda na'urar tantance masu zabe ta BVAS ta tantance.

An fadi sakamakon kananan hukumomi 16

Kara karanta wannan

Edo 2024: Zanga zanga ta barke kan sakamakon zabe, an samu bayanai

A baya mun wallafa yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke bayyana sakamakon zabe daga kananan hukumomi 18 na jihar Edo a babban birnin jihar.

Zuwa yanzu an bayyana sakamakon zaben da ya gudana a ranar Asabar daga kananan hukumomi 16, yanzu ana dakon alkaluman zaben daga kananan hukumomi biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.