Sakamakon Zaben Edo: Dan Takarar APC Ya Lallasa Na PDP a Karamar Hukumar Oshiomole
- Jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Edo a ƙaramar hukumar da Adams Oshiomole da Philip Shaibu suka fito
- Ɗan takarar APC a zaɓen Monday Okpebholo ya samu ƙuri'u 32,107 inda ya lallasa takwaransa na PDP, Asue Ighodalo wanda ya samu ƙuri'u 17,483
- Adams Oshiomole da Philip Shaibu sun taka rawar gani wajen ganin cewa ɗan takarar na APC ya samu nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Edo, Monday Okpebolo, ya samu nasara a ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma.
Ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma nan ne tsohon gwamnan jihar, Adam Oshiomhole da mataimakin gwamna Philip Shaibu suka fito.
APC ta yi nasara a ƙaramar hukumar Oshiomole
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Monday Okpebolo ya lallasa takwaransa na jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo a ƙaramar hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan takarar na APC ya samu ƙuri’u 32,107 yayin da takwaransa na PDP, Asue Ighodalo, ya samu ƙuri’u 17,483.
Philip Shaibu ya koma jam’iyyar APC ne gabanin zaɓen bayan ya daɗe yana gwabzawa tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki, wanda ya zaɓi Ighodalo a matsayin wanda yake son ya gaje shi.
Adams Oshiomole da Philip Shaibu na goyon bayan Monday Okpebholo domin ya zama gwamnan jihar Edo.
Karanta wasu labaran kan zaɓen Edo
- Sakamakon zaben Edo: Dan takarar PDP, Igholado ya samu nasara a karamar hukumarsa
- Sakamakon zaben Edo: APC ta lashe kananan hukumomi 10 yayin da PDP ta tsira da 6
- Edo: Yayin da ake sako sakamakon zabe, Gwamnonin APC sun koma ga Allah a bidiyo
APC ta lashe zaɓe a Esan
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC ) na ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo a babban ofishinta da ke birnin Benin.
Hukumar INEC ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zabe a karamar hukumar Esan ta Yamma da tazarar kuri'u 1,948.
Asali: Legit.ng