Tsohon Kwamishina a Kaduna Ya Zama Shugaban PDP, Ya Shirya Ɗaiɗaita APC
- Jam'iyyar PDP mai adawa reshen jihar Kaduna ta zabi tsohon kwamishina a matsayin sabon shugabanta
- Jam'iyyar ta zabi Edward Percy Masha a matsayin shugabanta bayan gudanar da zaben karkashin kulawar ma'aikatan INEC
- Baturen zabe daga hukumar, Tanko Beiji shi ya tabbatar da haka da safiyar yau Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Jam'iyyar PDP a jihar Kaduna ta zabi shugabanninta domin cigaba da jagorantarta.
Yayin zaɓen, tsohon Kwamishina a Kaduna, Edward Percy Masha ya yi nasarar zama shugaban jam'iyyar a jihar.
Kaduna: PDP ta zabi sababbin shugabanninta
Baturen zabe daga hukumar INEC, Barista Tanko Beiji shi ya bayyana haka a yau Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Beiji ya ce Masha ya samu kuri'u 2,123 yayin Danjuma Bello Sarki ya samu kuri'u 250 kacal a zaben.
An gudanar da zaben ne karkashin kulawar ma'aikatan INEC da jagororin PDP da yan jaridu a jihar.
Tsohon kwamishina ya zama sakataren PDP
Har ila yau, tsohon kwamishinan yada labarai, Alhaji Saidu Adamu ya zama sakataren jam'iyyar a jihar, Daily Post ta ruwaito.
Sannan Godiya Ayuba Lolo ta yi nasarar zama shugabar mata a jam'iyyar PDP da kuri'u 2,102 inda ta doke Angel Amadu da ke biye mata.
Tsohuwar mamban Majalisar dokoki, Hon. Mariya Dogo ita aka zaba a matsayin sakatariyar yada labarai na PDP.
PDP ta bukaci sauya AIG a Edo
Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi kira ga shugaban ƴan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun da ya janye mataimakinsa na shiyya ta bakwai.
PDP ta zargin cewa AIG Benneth Igwe ya haɗa baki da jam'iyyar APC domin ba ƴan daban jam'iyyar kariya su tayar da hargitsi.
Jam'iyyar ta buƙaci Kayode Egbetokun da ya gaggauta cire shi daga aikin zaɓen domin kaucewa samun rikici a jihar.
Asali: Legit.ng