Sakamakon Zaben Edo: APC Ta Lashe Kananan Hukumomi 11, PDP Ta Tsira da 6

Sakamakon Zaben Edo: APC Ta Lashe Kananan Hukumomi 11, PDP Ta Tsira da 6

  • Bayan karanta sakamakon zaben gwamnan Edo daga kananan hukumomi 16, jam'iyyar APC ta shiga gaban PDP da tazara mai yawa
  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa APC ta samu kuri'u 275,329 yayin da PDP ke biye da ita da kuri'u 220,892
  • A halin yanzu dai jam'iyyar APC ta yi rinjaye bayan lashe zabe a kananan hukumomi 11 inda PDP ta yi nasara a kananan hukumomi 6

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Farin ciki ya barka a tsakanin magoya jam'iyyar APC a Edo bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fadi sakamakon zaben kananan hukumomi 17.

Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar ta APC ta shiga gaban APC, LP da sauran jam'iyyu bayan karanta sakamakon kananan hukumomin 17.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Ana jiran karamar hukuma 1, APC ta ba PDP tazarar kuri'u sama da 50,000

Jam'iyyar PDP ta samu nasara a kananan hukumomi 10 yayin da PDP ke da 6
Edo 2024: APC ta shiga gaban PDP bayan da INEC ta fadi sakamakon kananan hukumomi 16. Hoto: @m_akpakomiza, @Aighodalo (X)
Asali: Facebook

APC ta lashe kananan hukumomi 10

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa APC ta samu jimillar kuri'u 275,329 yayin da PDP ke biye da ita da kuri'u 220,892 sai kuma ta ukunsu ita ce LP mai kuri'u LP: 13,348

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon zaben kanana hukumomi:

APC - 11

PDP - 6

LP - 0

INEC ta tafi hutun rabin lokaci

Bayan fadin sakamakon kanana hukumomi 13, hukumar INEC ta sanar da tafiya hutu inda ta ce za ta dawo ci gaba da fadin sakamakon da karfe 5:00 na yamma.

Jami'in tattara sakamakon zaben ya bayyana cewa za a tafi hutun ne saboda sauran jami'an kananan hukumomi biyu da suka rage na kan hanyarsu ta zuwa cibiyar.

Ana ci gaba da zaman dari dari a fadin jihar Edo yayin da magoya bayan jam'iyyar APC suka fara murna ganin cewa sun samu mafi rinjayen kuri'un da aka fadi.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Gwamna ya sha kaye a karamar hukumarsa, APC ta yi nasara

Duba wasu labarai kan zaben Edo:

Edo 2024: Dan takarar PDP ta samu nasara a karamar hukumarsa

Sakamakon zaben Edo: APC ta lashe karamar hukumar Esan ta Yamma

Akwai dalili: INEC ta yi barazanar soke zaben Edo da aka dora a IReV

"Wanda zai lashe zaben Edo" - Malami

Tun da fari, mun ruwaito cewa Prophet Joel Atuma na cocin The Lord Grace Provinces, Umuahia, jihar Abia, ya yi hasashen dan takarar da zai lashe zaben Edo.

Prophet Joel Atuma ya bayyana cewa akwai harafin 'E' a jikin sunan dan takarar da ya gano zai lashe zaben kuma ko kotu ba za ta iya sauya sakamakon zaben ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.