Sakamakon Zaben Edo: Dan Takarar PDP, Ighodalo Ya Samu Nasara a Karamar Hukumarsa
- Hukumar zabe ta INEC ta bayyana jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas ta Edo
- An rahoto cewa PDP ta samu kuri'u 14,199 inda ta doke jam'iyyar APC wadda ta samu kuri'u 8,398, yayin da Labour Party ta samu kuri'u 98
- Har yanzu dai hukumar INEC na ci gaba da tattarawa tare da sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka yi jiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar PDP Asue Ighodalo ya yi nasara a karamar hukumarsa ta Esan ta Kudu maso Gabas.
An bayyana hakan ne a yayin tattara sakamakon zaben jihar da jami’in baturen zabe, Farfesa Faruq Adamu Kuta, mataimakin shugaban jami’ar FUT da ke Minna ya jagoranta.
Ighodalo ya kawo karamar hukumarsa
PDP ta samu kuri'u 14,199 inda ta doke jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ta samu 8,398, yayin da Labour Party ta samu kuri'u 98, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga yadda sakamakon ya kasance:
Karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas na da gundumomin zabe 10.
APC - 8,398
PDP - 14,199
LP - 98
Mutanen da suka yi rijista - 90,240
Masu zabe da aka tantance - 23,390
Halartattun kuri'u - 22,780
Lalatattun kuri'u - 356
Gaba daya kuri'un da aka kada - 23,136.
Duba wasu labarai kan zaben Edo:
- Edo 2024: PDP ta lashe zabe a karamar hukumar Igueben da kuri'u 8470
- Sakamakon zaben Edo: APC ta lashe kananan hukumomi 10, PDP ta tsira da 6
- Zaben Edo: PDP, APC na zaman dari dari bayan INEC ta gaza fara tattara sakamako
EFCC ta cafke masu sayen kuri'u
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an hukumar EFCC sun cafke wasu mutane uku bisa zargin suna sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Edo.
An rahoto cewa mutanen da ke a wajen sun nuna turjuya lokacin da EFCC za ta tafi da wadanda aka kaman da suka hada da maza biyu da mace daya.
Asali: Legit.ng