Sakamakon Zaben Edo: PDP Ta ba APC Tazarar Kuri'u 2086 a Ovia ta Arewa maso Gabas
- A yayin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke ci gaba da bayyana sakamakon zaben Edo, PDP ta lashe Ovia ta Arewa maso Gabas
- An rahoto cewa PDP ta lashe zabe a karamar hukumar da kuri'u 15,311 inda ta ba jam'iyyar APC mai kuri'u 13,225 tazarar kuri'u 1,675
- Har yanzu dai INEC na ci gaba da bayyana sakamakon, inda kowacce jam'iyya ke da yakinin ita ce za ta lashe zaben gwamnan jihar ta Edo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Jam'iyyar PDP ta samu nasarar lashe zabe a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas da kuri'u 15,311 yayin da INEC ke bayyana sakamakon zaben jihar Edo.
Jami'in INEC da ke bayyana sakamakon karamar hukumar ya ce PDP ta samu kuri'u 13,225 yayin da mai bi mata Labour ta samu kuri'u 1,675.
Edo: PDP ta shiga gaban APC
Rahoton The Cable ya nuna cewa mutane 30,783 ne aka amince da kuri'unsu yayin da aka soke kuri'u 1,312 cikin kuri'u 32,095 da aka kada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga yadda sakamakon ya ke:
APC: 13,225
PDP: 15,311
LP: 1,675
Mutanen da suka yi rijista: 177,106
Masu zabe da aka tantance: 32,441
Halastattun kuri'u: 30,783
Lalatattun kuri'u: 1312
Gaba daya kuri'un da aka kada: 32,095
Duba wasu labarai kan zaben Edo:
- Edo 2024: APC ta shiga gaban PDP bayan lashe zabe a kananan hukumomi 10 cikin 16
- Sakamakon zaben Edo: Dan takarar PDP, Igholado ya samu nasara a karamar hukumarsa
- Zaben Edo: INEC ta soma fadin sakamako, PDP ta shiga gaban APC da kuri'u 8470
INEC ta yi barazanar soke zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce tana da hurumin soke duk wani sakamakon zabe da aka ayyana ta hanyar tursasawa.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a safiyar Lahadi awanni bayan kammala kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Edo.
Asali: Legit.ng