Edo 2024: APC Ta Lashe Esan Ta Yamma Yayin da INEC Ta Fara Tattara Sakamako
- Jam'iyyar adawa ta APC a jihar Edo ta samu nasarar lashe zabe a karamar hukumar Esan Ta Yamma bayan da INEC ta bayyana sakamako
- An rahoto cewa INEC ta bayyana APC a matsayin wadda ta lashe zabe a karamar hukumar da tazarar kuri'u 1,948 tsakaninta da PDP
- AN kada kuri'u 25,384 a karamar hukumar sai dai kuma kuri'u 24,691 ne kadai aka amince da su yayin da sauran kuri'un suka lalace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC ) na ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo a babban ofishinta da ke birnin Benin.
Hukumar INEC ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zabe a karamar hukumar Esan ta Yamma da tazarar kuri'u 1,948.
Edo: APC ta shiga gaban PDP
The Cable ta rahoto cewa APC ta samu kuri'u 12,952 yayin da PDP ta samu 11,004 sai kuma jam'iyyar LP da ta samu kuri'u 342.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga yadda sakamakon ya kasance:
APC: 12,952
LP: 342
PDP: 11,004
Mutanen da suka yi rijista: 113,067
Masu zaben da aka tantance: 25,702
Kuri'un da aka amince da su: 24,691
Kuri'un da suka lalace: 693
Kuri'un da aka kada gaba daya: 25,384
Duba wasu labarai kan zaben Edo:
- APC ta shiga gaban PDP bayan an fadi sakamakon kanana hukumomi 13
- INEC ta yi barazanar soke zaben jihar Edo da ta dora a IReV
- Zaben jihar Edo: EFCC ta cafke mutane hudu da laifin sayen kuri'u
Dalilin Obaseki na zuwa ofishin INEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa ya ziyarci ofishin hukumar INEC domin ganawa da baturen zabe na jihar.
Obaseki ya ce ya samu korafin cewa an hana wakilan PDP shiga cibiyar da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da ke a birnin Benin.
Asali: Legit.ng