Zaben Edo: INEC Ta Soma Fadin Sakamako, PDP Ta Shiga Gaban APC da Kuri'u 8470

Zaben Edo: INEC Ta Soma Fadin Sakamako, PDP Ta Shiga Gaban APC da Kuri'u 8470

  • Jam'iyyar PDP ta samu nasara a karamar hukumar Igueben yayin da hukumar INEC ta soma fadin sakamakon zaben jihar Edo
  • An rahoto cewa jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 8, 470 yayin da APC ke binta a baya da kuri'u 5,907 da kuma LP mai kuri'u 494
  • A ranar Asabar, 21 ga watan Satumbar 2024 ne al'ummar jihar Edo suka fita kwansu da kwarkatarsu domin zaben sabon gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar da fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a jiya Asabar.

Hukumar ta fara soma fadin sakamakon zaben karamar hukumar Igueben inda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 8470 wanda ya ba ta nasara kan sauran jam'iyyu.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: PDP ta ba APC tazarar kuri'u 2086 a Ovia ta Arewa maso Gabas

PDP ta samu nasara a karamar hukumar Igueben
Zaben Edo: INEC ta fara tattara sakamakon zabe, PDP ta yi nasara. Hoto: @Aighodalo
Asali: Facebook

PDP ta lallasa APC a Igueben

Rahoton Channels TV ya nuna cewa APC ta samu kuri'u 5,907 yayin da jam'iyyar Labour ta samu kuri'u 494.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga yadda sakamakon ya kasance:

APC - 5,907

PDP- 8,470

LP - 494

Mutanen da suka yi rijista - 54,549

Wadanda aka tantance - 15,274

Kuri'un da aka kada - 15, 267

Kuri'un da aka amince da su - 14,989

Lalatattun kuri'u - 278

An bayyana cewa wannan ita ce karamar hukumar farko da hukumar INEC ta bude fadin sakamakon zaben jihar Edo da ita.

Duba labarai kan zaben Edo:

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben jihar Edo: PDP ta lallasa APC a karamar hukumar Uhunmwonde

INEC ta yi barazanar soke zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi barazanar soke duk wani sakamakon zaben jihar Edo da aka dora a shafinta na IReV ma damar ya saba doka.

INEC ta ce idan har ta gano cewa an tursasa jami'inta wajen ayyana sakamakon zaben, to ba makawa za ta yi amfani da karfin ikonta na soke sakamakon zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.