Edo 2024: INEC Ta Gargadi Gwamna Obaseki, Ta Koka da Halin Yan Siyasa

Edo 2024: INEC Ta Gargadi Gwamna Obaseki, Ta Koka da Halin Yan Siyasa

  • Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta nuna damuwa kan yadda wasu yan siyasa suka cika ofishinta a jihar Edo
  • Hukumar ta yi Allah wadai da lamarin bayan ziyarar Gwamna Godwin Obaseki da wasu yan siyasa da suka yi zanga-zanga
  • Hukumar ta yi gargadi mai karfi game da lamarin inda ta ce ba za ta bari a kawo tsaiko game da tattara sakamakon zaben ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Hukumar zabe ta INEC ta gargadi Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.

Hukumar ta yi wannan gargadi ne bayan gwamnan ya je ofishinta da ake shirin fara tattara sakamakon zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: PDP, APC na zaman dari dari bayan INEC ta gaza fara tattara sakamako

INEC ta yi magana bayan Obaseki ya je ofishinta da tsakar dare
Hukumar ta yi Allah wadai da halin yan siyasa bayan cika ofishinta a jihar Edo. Hoto: Governor Godwin Obaseki, INEC.
Asali: Twitter

Edo: INEC ta gargadi yan siyasa

Kwamishinan Tarayya a hukumar, Mallam Mohammed Haruna shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daily Trust ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haruna ya koka kan lamarin inda ya ce abin takaici ne yadda yan siyasa suka ziyarci ofishin da tsakar dare.

"Ba mu ji dadi ba game da cika ofishinmu da kuma zanga-zanga da aka yi ana shirin fara sanar da sakamakon zabe."
"Wannan abin takaici ne kuma bai kamata a hargitsa shirin tattarawa da kuma sanar da sakamakon zaben ba."

- Mallam Mohammed Haruna

INEC ta roki jami'an tsaro a zaben Edo

Haruna ya bukaci jami'an tsaro su cigaba da ba da kariya ga al'umma kamar yadda iska saba.

Ya ce ya kamata a ba wakilan jam'iyyu da masu kula da zaɓe da kuma yan jaridu dama game da duka wuraren tattara sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

Edo: Ana shirin fadin sakamakon zaben gwamna, 'Yan sanda sun kara matakan tsaro

Wannan na zuwa ne yayin da aka fara tattara sakamakon zaben jihar da aka yi a jiya Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.

Gwamna Obaseki ya ke ofishin INEC

Kun ji cewa Ganin Gwamna Godwin Obaseki na Edo a wurin tattara sakamakon zabe na INEC a jihar ya tayar da kayar baya.

Jam'iyyar APC ta fusata da ganin Gwamna Obaseki a ofishin INEC da tsakar dare inda ta bukaci ya bar wurin.

Mataimakin dan takarar gwamnan APC, Dennis Idahosa ya ce dole Obaseki ya bar ofishin saboda bai da alaka da wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.