Zaben Edo: Dan Takarar PDP Ya Fara Karaya, Ya Zargi Hukumar INEC

Zaben Edo: Dan Takarar PDP Ya Fara Karaya, Ya Zargi Hukumar INEC

  • Ɗan takarar gwamnan PDP a zaɓen jihar Edo ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da zaɓen
  • Asue Ighodalo ya yi zargin cewa an samu tafka maguɗi da aringizon ƙuri'u a wurare da dama da aka gudanar da zaɓen
  • Ɗan takarar na PDP ya bayyana cewa zaɓen ya kama hanyar zama mafi muni a tarihin Najeriya saboda zarge-zargen tafka maguɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Ɗan takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo, ya nuna damuwarsa kan zaɓen gwamnan.

Asue Ighodalo ya yi gargaɗin cewa za a iya tunawa da zaɓen a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya saboda zarge-zargen tafka maguɗi.

Ighodalo ya koka kan zaben Edo
Asue Ighodalo ya nuna damuwa kan zaben gwamnan Edo Hoto: Asue Ighodalo - AI Comms
Asali: Facebook

Vanguard ta ce Ighodalo ya yi wannan ikirarin ne yayin wani taron manema labarai a ranar Lahadi, wanda ƙungiyar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP na jihar Edo, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ta shirya.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: INEC ta sanar da lokacin ci gaba da tattara sakamako

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron wanda ya samu halartar gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya mayar da hankali ne kan zargin maguɗi da hukumar zaɓe ta INEC ta yi, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Wane zargi ɗan takarar PDP ya yi?

"Yadda wannan zaɓen ke gudana, yana shirin zama zaɓe mafi muni a tarihin ƙasar nan."

- Asue Ighodalo

Ya yi nuni da rumfunan zaɓe da dama da aka samu maguɗin zaɓe, inda ya nuna shakku kan sakamakon zaɓen da ake sanarwa.

Ɗaya daga cikin maguɗin da ya yi misali da shi, shi ne na rumfar zaɓe a Ikpoba/Okha Ologbo, inda ba a tantance masu kaɗa ƙuri'a ko mutum ɗaya ba amma an sanar da sakamakon zaɓe.

"A Ikpoba/Okha Ologbo, babu adadin waɗanda aka tantance domin kaɗa ƙuri'a, amma sakamakon ya nuna APC ta samu ƙuri'u 227, PDP ta samu 104. Ta yaya hakan zai faru?"

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Dan takarar PDP ya fadi wanda zai yi nasara da gagarumin rinjaye

- Asue Ighodalo

INEC ta yi barazanar soke sakamako

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce tana da hurumin soke duk wani sakamakon zabe da aka ayyana ta hanyar tursasawa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a safiyar Lahadi, 22 ga watan Satumban 2024, awanni bayan kammala kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng