Edo: Ana Shirin Fadin Sakamakon Zaben Gwamna, 'Yan Sanda Sun Kara Matakan Tsaro
- Magoya bayan jam'iyyu a Edo, yan siyasa da jama'ar gari na dakon a fadi sakamakon zaben gwamnan jihar
- Tuni shirye-shirye su ka yi nisa, wanda ya sa rundunar yan sandan kasar nan ta tsaurara tsaro a Benin da kewaye
- An kara yawan yan sanda da sauran matakan da za su tabbatar da an bi doka yayin da INEC ke sanar da sakamakon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Edo - Yayin da aka kammala zaben gwamna a kananan hukumomi 18 na Edo, an fara shirin bayyana sakamakon zaben. Mutane sama da miliyan 2.2 suka cancanci fito wa kada kuri'arsu, amma kasa da 40% ne su ka yi zaben na ranar Asabar.
BBC Hausa ta wallafa cewa an kara jibge jami'an yan sanda a babban birnin jihar, Benin gabanin bayyana sakamakon zaben.
Zabe: An kara jami'an tsaro a Edo
Rundunar yan sandan kasar nan ta kara yawan jami'an tsaro a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke birnin Benin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin ya biyo bayan shirye-shiryen da ake yi na fadin sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.
An jibge karnuka a ofishin INEC a Edo
Daga cikin matakan tsaro da rundunar yan sanda ta dauka akwai karin karnuka masu horo a birnin Edo da kewaye. An dauki matakin ne domin taimaka wa jami'an tsaro wajen tabbatar da tsaro yayin da ake tattara sakamakon zaben gwamna daga mazabu a babban ofishin INEC da ke Benin.
Gwamnan Edo ya fadi dalilin zuwa ofishin INEC
A baya mun ruwaito cewa gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya fuskanci fushin yan sanda bayan ya ziyarci ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) yayin da zaben gwamna ke gudana a jihar.
Lamarin ya sa yan jam'iyyar adawa na APC tsunduma zanga-zanga bisa zargin za a iya yi masu rashin adalci, amma gwamnan ya ce gaza samun INEC a waya ne ya tilasta masa kai ziyarar.
Asali: Legit.ng