Zaben Edo: Bayan An Kunyata Shi, Gwamna Ya Fadi Dalilin Kai Ziyara Ofishin INEC

Zaben Edo: Bayan An Kunyata Shi, Gwamna Ya Fadi Dalilin Kai Ziyara Ofishin INEC

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayyana dalilin da ya sa ya kai ziyara ofishin baturen zabe (REC) na jihar da safiyar Lahadi
  • An rahoto cewa zanga zanga ta barke daga magoya bayan jam'iyyar APC a jihar bayan samun labarin cewa Obaseki ya ziyarci INEC
  • Sai dai Gwamna Obaseki ya ce ya ziyarci ofishin INEC ne kawai domin duba yadda lamura ke tafiya bayan gaza samun hukumar a waya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Godwin Obaseki ya ce ya ziyarci cibiyar tattara sakamako ta INEC da ke a jihar ne domin ya samu bayanai na farko game da yadda abubuwa ke tafiya.

Gwamnan jihar Edo ya dura ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) a garin Benin da sanyin safiya, inda ya samu turjiya daga jami'an 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Ana tsaka da kada kuri'a, 'yan bindiga sun yi awon gaba da akwatin zabe

Gwamna Godwin Obaseki ya yi magana kan dalilin ziyartar ofishin INEC
Zaben Edo: Gwamna Obaseki ya yi martani kan zuwansa ofishin INEC da safiyar Lahadi. Hoto: @GovernorObaseki
Asali: Twitter

Gwamna ya ziyarci ofishin INEC

Channels TV ta rahoto cewa Gwamna Obaseki ya kai ziyara ofishin INEC ne da sanyin safiyar ranar Lahadi awanni bayan kammala kada kuri'a a zaben jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan wanda ya samu rakiyar mataimakansa na tsaro, ya shiga ofishin baturen zabe na INEC (REC) inda suka yi wata tattaunawa da ta dauki sama da awa daya.

Obaseki ya bar ofishin INEC da misalin karfe 4:45 na safe, ko da yake jami’an tsaronsa sun hana ‘yan jarida yin magana da shi.

Dalilin zuwan Obaseki ofishin INEC

Da ya ke martani kan dalilin kai ziyara ofishin INEC, The Punch ta rahoto gwamnan na cewa ya dura ofishin ne saboda gaza samun damar yiwa baturen zaben magana.

Gwamnan ya ce ziyarar tasa ta biyo bayan gaza tuntubar hukumar zaben a kokarin jin ta bakin baturen zabe (REC) na jihar, Anugbum Onuoha.

Kara karanta wannan

Edo: APC ta kadu da ganin Gwamna Obaseki a INEC, yan sanda sun dauki mataki

Ya ce:

“Da misalin karfe 1, na samu rahoton cewa an sauya wurin tattara sakamakon zaben zuwa babban ofishin INEC, kuma har ma an hana wakilan PDP shiga dakin taron.
A wannan lokacin, na kira baturen zaben domin neman bayanin abin da ke faruwa ban same shi ba, wannan ya sa na je ofishin INEC domin ganawa da shi."

Duba wasu labarai kan zaben Edo:

INEC ta manta takardar sakamako

A wani labarin, mun ruwaito cewa rigima ta barke a wata rumfar zabe a gundumar Orhionmwon da ke a karamar hukumar Orhionmwon, jihar Edo.

Matasan rumfar sun tayar da tarzoma cewa ba za a ci gaba da kada kuri'a ba bayan da suka gano cewa jami'an INEC sun manta da takardar rubuta sakamako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.