Edo 2024: Ana Tsaka da Kada Kuri'a, 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Akwatin Zabe

Edo 2024: Ana Tsaka da Kada Kuri'a, 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Akwatin Zabe

  • 'Yan bindiga sun kwacewani akwatin zabe a Owan ta Yamma a lokacin zaben gwamnan jihar Edo a 2024, a cewar wani jigon PDP
  • 'Yan bindigar dauke da makamai sun kawo cikas wajen kada kuri’a, lamarin da ya haifar da fargaba game da tsaro a zaben jihar
  • Barista Godwin Dudu-Orumen ya bukaci INEC da ta binciki lamarin tare da tabbatar da sahihancin zaben a yankin da abin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Edo - Wani jigo a jam’iyyar PDP, Barista Godwin Dudu-Orumen, ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun hargitsa zabe a karamar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo ranar Asabar.

A cewar Dudu-Orumen, ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin rumfar zabe, inda suka kwace akwatin zabe, sannan suka arce daga wurin.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a cin hancin N10000’

Jigon PDP ta yi magana kan sace akwatin zabe a jihar Edo
Edo: Jigon APC ya kokawa INEC bayan ikirarin cewa an sace wani akwatin zabe a Owan. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Edo: An sace akwatin zabe

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa lamarin da ya faru duk da sauraran matakan tsaro a fadin jihar ya haifar da fargaba kan yadda zaben ke gudana a yankin da lamarin ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya nuna rashin jin dadinsa da faruwar lamarin, inda ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su gaggauta daukar matakin kwato akwatin zabe da aka sace.

Yayin da INEC ba ta ce uffan ba a hukumance kan lamarin, Dudu-Orumen ya bukaci hukumar da ta gudanar da cikakken bincike tare da daukar matakan da suka dace kan lamarin.

An rahoto cewa akwai wurare da dama da aka gudanar da zabe cikin lumana a Edo yayin da wasu wuraren aka samu tashin hankula.

Duba wasu labarai kan zaben Edo

KARANTA: Sakamakon zaben Edo daga gundumomi da kananan hukumomi

Kara karanta wannan

Edo 2024: INEC ta tsawaita lokutan zabe, ta fadi musabbabin ɗaukar matakin

EFCC ta cafke masu sayen kuri'u a yayin da ake zaben gwamnan jihar Edo

Rigima ta barke a rumfar zabe bayan INEC ta manta da takardar sakamako

Edo: An tafka sayen kuri'u

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kungiyar Yiaga Africa ta nuna damuwa kan cewa zaben gwamnan Edo na cike da sayen kuri'u da sauran laifuffukan zabe.

Yiaga Africa ta yi ikirarin cewa wakilan PDP da APC sun ba masu kada kuri'a cin hancin N10,000 a Igueben-Idumoka (12-10-03-004) a karamar hukumar Igueben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.