Zaben Edo: 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki bayan Gwamna Ya Dira a Ofishin INEC
- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya je harabar ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da ke birnin Benin cikin tsakar dare
- Jami'an ƴan sandan ƙarƙashin jagorancin DIG Frank Mba sun yi waje da gwamnan bayan ya kwashe wani lokaci a cikin harabar
- Tun da farko mambobin APC sun nuna adawa kan kasancewar gwamnan a harabar ofishin na hukumar INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - DIG Frank Mba ya tilastawa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo fita daga harabar ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da ke Benin.
Gwamna Obaseki dai yaje harabar ne da daddare misalin ƙarfe 2:00 na dare kuma yana nan har sai da ƴan sanda suka yi masa rakiya zuwa waje.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa Gwamna Obaseki ya je ofishin na INEC domin ya yi ƙorafi kan wasu kura-kurai da aka yi wajen tattara sakamakon zaɓen gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobin jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin abokin takarar Monday Okpebolo, Dennis Idahosa, sun jagoranci masu zanga-zangar neman ficewar Obaseki daga harabar da misalin ƙarfe 3:30 na dare.
Ƴan sanda sun kori Gwamna Obaseki
Da wajen misalin ƙarfe 3:00 na dare tawagar jami'an ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin Frank Mba da sojoji suka shiga harabar ofishin na INEC, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Zuwa ƙarfe 4:00 na dare tawagar jami'an tsaron sun fitar da gwamnan daga harabar ofoshin na INEC.
Yayin da ake fitar da shi daga harabar, ƴan sandan tafi da gidanka da aka tura ofishin INEC sun riƙa gayawa gwamnan cewa "fita, fita."
Mintoci kaɗan kafin Frank Mba ya jagoranci Obaseki waje tare da tawagar ƴan sanda, sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Surajudeen Basiru, ya yi wa manema labarai jawabi cewa gwamnan ba shi da wani dalili na kasancewa a harabar.
Ƴan sanda sun magantu kan zaɓen Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin Sufeto-Janar na ƴan sanda (DIG) Frank Mba ya bayyana cewa jama’a sun fito domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar Edo.
Frank Mba, wanda ke kula da ayyukan tsaro a zaɓen, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, 21 ga Satumba, 2024.
Asali: Legit.ng