Edo: APC Ta Kadu da Ganin Gwamna Obaseki a INEC, Yan Sanda Sun Dauki Mataki

Edo: APC Ta Kadu da Ganin Gwamna Obaseki a INEC, Yan Sanda Sun Dauki Mataki

  • Ganin Gwamna Godwin Obaseki na Edo a wurin tattara sakamakon zabe na INEC a jihar ya tayar da kayar baya
  • Jam'iyyar APC ta fusata da ganin Gwamna Obaseki a ofishin INEC da tsakar dare inda ta bukaci ya bar wurin
  • Mataimakin dan takarar gwamnan APC, Dennis Idahosa ya ce dole Obaseki ya bar ofishin saboda bai da alaka da wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Mataimakin dan takarar APC a zaben Edo, Dennis Idahosa ya nuna damuwa bayan zuwan Gwamna Obaseki wurin tattara sakamakon zabe.

Idahosa ya bukaci gwamnan da ya bace daga harabar tattara sakamakon zaben da INEC ta ke yi.

APC ta nuna damuwa bayan ganin Obaseki a ofishin INEC da tsakar dare
Jam'iyyar APC ta bukaci Gwamna Godwin Obaseki ya yi gaggawar ficewa daga ofishin INEC. Hoto: Monday Okpebholo, Olumide Akpata, Asue Ighodalo.
Asali: Getty Images

APC ta fusata da Obaseki a ofishin INEC

Kara karanta wannan

Akwai dalili: INEC ta yi barazanar soke sakamakon zaben Edo da aka dora a IReV

Punch ta ruwaito cewa Obaseki ya isa wurin tattara sakamakon ne da misalin karfe 3:30 na daren yau Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin dan takarar gwamnan ya yi ta ihu daga bakin mashigar inda ya ce babu dalilin kasancewar gwamnan a wannan wuri.

Ya ce dole Obaseki ya fita daga harabar saboda bai kamata a ce yana can ba domin shi ba ma'aikacin INEC ba ne, cewar Vanguard.

"Dole Obaseki ya bace daga wurin, shi ba ya aiki da hukumar INEC, bai kamata rundunar yan sanda ta bari ba."

- Dennis Idahosa

Mambobin APC sun cika ofishin INEC

Mambobin jam'iyyar APC da ke wurin da suka nuna rashin jin dadinsu sun yi kokarin shiga harabar amma an hana su shiga.

Daga bisani an gano mataimakin sifetan yan sanda da ke kula da zaben, Frank Mba ya shigo harabar tare da zuwa inda Obaseki ke zaune.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Bayan an kunyata shi, gwamna ya fadi dalilin kai ziyara ofishin INEC

INEC ta magantu kan sakamakon zaben Edo

Kun ji cewa Hukumar zabe ta INEC ta musanta fara sanar da sakamakon zaben jihar Edo da aka gudanar a yau Asabar.

INEC ta ce duk wani sakamakon zabe da ake yadawa ba daga gare ta yake ba saboda ba ta fara tattara sakamakon ba.

Wannan na zuwa ne bayan wasu mutane sun yi ta yada sakamakon zabe da aka ce daga hukumar zaben suke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.