Edo: INEC Ta Magantu kan Fara Sanar da Sakamakon Zabe, Ta Fadin Hali da Ake Ciki
- Hukumar zabe ta INEC ta musanta fara sanar da sakamakon zaben jihar Edo da aka gudanar a yau Asabar
- INEC ta ce duk wani sakamakon zabe da ake yadawa ba daga gare ta yake ba saboda ba ta fara tattara sakamakon ba
- Wannan na zuwa ne bayan wasu mutane sun yi ta yada sakamakon zabe da aka ce daga hukumar zaben suke
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta yi magana kan fara fitar da sakamakon zabe a jihar Edo.
INEC ta ce ba ta fara karbar sakamakon zabe daga kananan hukumomi 18 ba a jihar a zaben da aka gudanar.
Edo: INEC ta yi magana kan sakamakon zabe
Kwamishinan INEC a jihar, Anugbum Onuoha shi ya fadi haka yayin hira da Channels TV a yau Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onuoha ya ce har yanzu ana cigaba da tattara sakamakon zaben ne a matakin unguwa tukun.
Ya koka kan yadda wasu suke ta yada sakamakon zaben jihar na karya inda ya ce kwata-kwata ba daga hukumar ba ne.
"Ba zan iya fadar lokacin da za mu fara sanar da sakamakon zaben ba, saboda duk lokacin da suka zo, za mu sanar."
"Ina son yin gyara a wani abu daya, wadanda suke yada cewa mun sanar da sakamako ba daga gare mu ba ne."
"INEC ba ta sanar da sakamakon zabe ba, ba ni ne mai sanarwa ba, mai sanarwar zai sanar, amma na yi mamaki abin da na ke gani a kafofin sadarwa."
- Anugbum Onuoha
Edo: PDP ta yi korafi kan cin zarafi
Kun ji cewa yayin da ake cigaba da zaben jihar Edo, dan takarar jam'iyyar PDP ya yi korafi kan yadda lamura ke tafiya a yankinsa.
Asue Ighodalo ya zargi jami'an tsro da cafke magoya bayan PDP ba tare da sun yi wani laifi na saba doka ba a zaben.
Ighodalo ya kuma nuna damuwa kan yadda hukumar INEC ta yi jinkiri wurin kawo kayan aikin zabe a inda ya fi karfi.
Asali: Legit.ng