An Tona Yadda Aka Yi Amfani da Burodi Aka Saye Kuri’un Jama’a a Zaben Gwamnan Edo

An Tona Yadda Aka Yi Amfani da Burodi Aka Saye Kuri’un Jama’a a Zaben Gwamnan Edo

  • Gungun kungiyoyi na Nigeria Civil Society Situation Room (NCSSR) sun ce an saye kuri’un talakawa a zaben Edo
  • A yau Asabar ne dubban al’umma su ka fito domin kada kuri’arsu a zabi wanda zai zama sabon gwamna a jihar Edo
  • Kungiyoyin da ke sa ido a al’amuran zabe sun ce an yaudari mutane da abinci, burodi da kudi domin saida kuri’arsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Edo - Gungun kungiyoyi masu zaman kansu sun yi zargin cewa an saye kuri’un mutane a zaben sabon gwamnan jihar Edo.

Bayanan sun bata nagartar zaben gwamnan wanda aka sa ran cewa INEC da sauran hukumomin tarayya za su tabbatar da adalci.

Zaben Gwamnan Edo
Jam'iyyu sun ba da burodi domin sayen kuri'u a zaben Gwamna a jihar Edo Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

An saye kuri'u a zaben gwamnan Edo

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a cin hancin N10000’

Kungiyar NCSSR ta masu sa ido a zabe ta yi ikirarin cewa an saye kuri’un jama’a a zaben Edo, Daily Trust ce ta kawo rahoton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin NCSSR sun ce karara aka rika sabawa ka’idojin zabe, ana amfani da dukiya domin a canza zabin al’ummar Edo.

Kungiyar ta ce duk da an baza jami’an tsaro a jihar Edo, wannan bai hana a saye kuri’un masu kada zabe a wasu rumfuna ba.

Yunusa Z. Ya’u, Mimidoo Achakpa da Franklin Oloniju suka fitar da wata sanarwa da sa hannunsu inda suka bayyana hakan dazu.

Yayin da yanzu ake jin sakamako a rumfunan Edo, kungiyar ta ce an saye kuri’un mutane da kudi tun daga N5000 har zuwa N1000.

"A wasu wuraren kuwa, NCSSR ta bayyana cewa an ba da kayan abinci ne tun daga burodi da makamantansu domin samun kuri’a."

Kara karanta wannan

Edo 2024: Ɗan takarar PDP ya koka, ya hango wata matsala ana tsaka da zaɓe

"Farashin kuri’u ya fara ne daga N5000 zuwa N10, 000 a wurare da yawa."

- Inji NCSSR

Wuraren da aka saye kuri'u a Edo

"Daga cikin wuraren akwai rumfa ta PU08 da PU09 da ke karamar hukumar Owan ta Gabas a Edo.

"Akwai rumfa ta PU 02 a karamar hukumar Etsa ta Yamma da wasu rumfuna da yawa a Egor, Oredo da Owan ta gabas."

-NCSSR

Asirin masu sayen kuri'u ya tonu

Sai dai a karamar hukumar Oredo, kungiyar ta yarda an yi ram da wasu mutane da ake zargin masu sayen kuri’a ne wajen zaben.

Kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto gungun ya kunshi kungiyoyi kamar PLAC, CDD, CITAD, YIAGA Africa da kuma TAF Africa.

Sauran kungiyoyin nan sun kunshi RULAAC, DAG, JONAPWD, NISD, CPI, CHEDA da wata kungiya da ke ba mata damar yin karatu.

Edo 2024: YIAGA ta ce an saye kuri'u

Dazu aka samu labari cewa kungiyar Yiaga Africa ta zargi wakilan jam'iyyar APC da PDP da sayen kuri'u domin zama gwamnan Edo.

Yiaga ta lissafa kananan hukumomin da ta ce an fi samun sayen kuri'u, a wasu wuraren ana ba da N10,000 domin su dangwala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng