Edo 2024: INEC Ta Tsawaita Lokutan Zabe, Ta Fadi Musabbabin Ɗaukar Matakin
- Yayin da aka samu matsaloli da dama yayin zaben jihar Edo, hukumar INEC ta tsawaita lokutan zabukan
- Hukumar ta ba da dalilai kamar na ruwan sama da kuma rashin kawo kayan gudanar da zaben a kan lokaci
- Inda abin ya shafa akwai mazabar dan takarar gwamnan PDP, Asue Ighodalo da ke Ward 1 a Ewohimi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Hukumar zabe a Edo ta tsawaita lokutan gudanar da zabuka a wasu wurare a jihar.
Wannan matakin bai rasa nasaba da jinkiri da aka samu da kuma ruwan sama a wasu wurare yayin zaben.
Edo: Hukumar INEC ta tsawaita lokutan zabe
Daily Trust ta ruwaito cewa an samu matsaloli da dama a wasu wurare da suka kawo tsaiko game da zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A mazabar Ward 1 a Ewohimi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa an samu jinkirin zuwan kayan zaɓe.
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo na daya daga cikin wadanda ke kada kuri'a a mazabar.
Dan takarar PDP a zaben Edo ya koka
Ighodalo ya koka kan yadda aka samu matsalar tare da zargin ana neman kassara shi a yankinsa.
Dan takarar ya wasu daga cikin magoya bayan PDP da aka cafke babu abin da suka aikata saboda suna bakin layin zabe ne.
Ya bukaci hukumar zabe ta INEC da ta kara wa'adin zaben a yankin Ewohimi bayan zabga ruwan sama da ya kawo cikas a zaben.
INEC ta magantu kan rashawa a Edo
Kun ji cewa Yayin da aka fara kada kuri'a a zaben jihar Edo, kwamishinar zabe ta bayyana shirin hukumar domin yin adalci.
Farfesa Rhoda Gumus ta ce ko nawa aka kawo mata na cin hanci ba za ta taɓa karba ba domin kare mutuncinta da kimarta.
Farfesa Gumus ta ce ko kusa babu wanda ke da karfin halin da zai tunkare ta game da cin hanci ko biliyan nawa za a ba ta domin sauya mata tunani.
Asali: Legit.ng