Zaben Edo: Oshiomole Ya Yi Martani kan Zargin APC Na Siyan Kuri'u

Zaben Edo: Oshiomole Ya Yi Martani kan Zargin APC Na Siyan Kuri'u

  • Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomole ya yi martani kan zargin cewa APC na siyan ƙuri'u a zaɓen gwamnan jihar
  • Oshiomole ya musanta zargin wanda ya bayyana a matsayin abin dariya domin a cewarsa APC ba ta raba kuɗi a zaɓen
  • Oshiomole ya bayyana cewa jama'a suna zaɓar jam'iyyar APC ne domin suna son su samu jagoranci na gari a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomole, ya yi magana kan zargin APC ta shirya siyan ƙuri'u a zaɓen gwamnan jihar.

Adams Oshiomole ya musanta zargin cewa jam'iyyar ta tanadi tulin kuɗi domin amfani da su wajen siyan ƙuri'u a hannun mutane a lokacin zaɓen.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Gwamna ya kaɗa ƙuri'a, ya aika saƙo mai muhimmanci ga hukumar INEC

Oshiomole ya musanta siyan kuri'a a zaben Edo
Oshiomole ya musanta zargin APC za ta siya kuri'u a zaben Edo Hoto: Adams Oshiomole
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Oshiomole ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓe ta ɗaya a mazaɓa ta 10 cikin ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Oshiomole ya yi?

Oshiomole wanda shi ne sanatan Edo ta Arewa ya bayyana cewa bai samu rahoton tashin hankali yayin da ake gudanar da zaɓen ba.

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya kuma bayyana cewa ana kaɗa ƙuri'a cikin kwanciyar hankali a zaɓen.

"Abin dariya ne idan na ji irin wannan zargin. Kun zo wajen zaɓen, shin kun ga a inda ake raba kuɗi? Mutane sun fito domin su zaɓe mu saboda suna son jagoranci mai kyau."
"A lokacin yaƙin neman zaɓen mu, mutane sun fito domin su ganni ba wai saboda zan ba su wani abu ba, amma saboda abin da na yi musu a lokacin da nake a matsayin gwamna."

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Dan takarar APC ya cika baki bayan ya kammala kada kuri'a

- Adams Oshiomole

Ɗan takarar APC ya cika baki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yiwa abokin hamayyarsa na PDP shaguɓe.

Sanata Monday Okpebholo ya cika da baki kan cewa abokin hamayyarsa na PDP, Asue Ighodalo, ba zai samu ƙuri'a ko ɗaya ba a rumfar zaɓensa da ke mazaɓa ta ɗaya a Uwessa cikin ƙaramar hukumar Esan ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng