Edo 2024: PDP Ta Fara Korafi, Dan Takara Ya Fadi Makircin da APC Ta Shirya
- Yayin da ake cigaba da zaben jihar Edo, dan takarar jam'iyyar PDP ya yi korafi kan yadda lamura ke tafiya a yankinsa
- Asue Ighodalo ya zargi jami'an tsro da cafke magoya bayan PDP ba tare da sun yi wani laifi na saba doka ba a zaben
- Ighodalo ya kuma nuna damuwa kan yadda hukumar INEC ta yi jinkiri wurin kawo kayan aikin zabe a inda ya fi karfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben jihar Edo, Asue Ighodalo ya yi korafi kan abubuwan da ke faruwa.
Ighodalo ya nuna damuwa kan yadda jami'an tsaro ke kama magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar.
Edo" Dan takarar PDP ya zargi jami'an tsaro
Premium Times ta ruwaito Ighodalo na fadin haka a mazabarsa da ke Ewohimi da ke karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan takarar ya bayyana haka ne bayan kada kuri'a da misalin karge 10:40 na safe a yau Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.
Ighodalo ya wasu daga cikin magoya bayan PDP da aka cafke babu abin da suka aikata saboda suna bakin layin zabe ne, cewar Punch.
Dan takarar PDP ya zargi shirin nakasa shi
Ya kuma bayyana samun wani rahoto cewa an samu jinkiri wurin fara gudanar da zabe a wuraren da yafi karfi a jihar.
"An tsayar da zabe har na fiye da awanni biyu a wuraren da na ke da karfi sosai."
- Asue Ighodalo
Ighodalo ya bukaci hukumar zabe ta INEC da ta kara wa'adin zaben a yankin Ewohimi bayan zabga ruwan sama da ya kawo cikas a zaben.
INEC ta magantu kan rashawa a Edo
Kun ji cewa yayin da aka fara kada kuri'a a zaben jihar Edo, kwamishinar zabe ta bayyana shirin hukumar domin yin adalci.
Farfesa Rhoda Gumus ta ce ko nawa aka kawo mata na cin hanci ba za ta taɓa karba ba domin kare mutuncinta.
Farfesa Gumus ta ce ko kusa babu wanda ke da karfin halin da zai tunkare ta game da cin hanci ko biliyan nawa ne.
Asali: Legit.ng