Zaben Edo: Dan Takarar APC Ya Cika Baki bayan Ya Kada Kuri'a

Zaben Edo: Dan Takarar APC Ya Cika Baki bayan Ya Kada Kuri'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Edo - Ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yiwa abokin hamayyarsa na PDP shaguɓe.

Sanata Monday Okpebholo ya cika da baki kan cewa abokin hamayyarsa na PDP, Asue Ighodalo, ba zai samu ƙuri'a ko ɗaya ba a rumfar zaɓensa da ke mazaɓa ta ɗaya a Uwessa cikin ƙaramar hukumar Esan ta Tsakiya.

Monday Okphebolo ya sha alwashi kan zaben Edo
Monday Okpebholo ya ce ya yi magana kan zaben Edo Hoto: @Aighodalo, @m_akpakomiza
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Okpebholo ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen.

"PDP ko wani can daban ba za su samu ko ƙuri'a ɗaya ba a nan, saboda nan gida na ne kuma mutane na suna sona."

Kara karanta wannan

Zaben Edo: PDP ta bukaci IGP ya janye babban jami'in 'yan sanda, ta fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Sanata Monday Okpebholo

Okpebholo ya kuma yabawa hukumar zaɓe ta INEC kan yadda ake gudanar da zaɓen inda ya bayyana cewa hukumar ta yi abin da ya dace.

Da aka tambaye shi kan jami'an tsaron da aka turo domin zaɓen, ya bayyana cewa babu wata matsalar tsaro da aka fuskanta.

"Na san cewa duk surutu ne kawai suke yi kan tsaro. Duba ku gani babu abin da ya faru. Kuna iya gani dai babu wanda yake yin faɗa, ba ƙarar fashe-fashe ko wani abu daban."
"Domin haka surutu kawai suka riƙa yi domin su firgita mutane ka da su yi zaɓe."
"Kun san cewa Obaseki yana son ya kunna wuta a jihar Edo, amma cikin ikon Allah komai yana tafiya daidai."

- Sanata Monday Okpebholo

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng